Da Dumi Dumi

’Yan siyasa ku bar bata juna ku gina kasa – Isyaku Ibrahim

Alhaji Isyaku Ibrahim
Alhaji Isyaku Ibrahim

Ma’ajin rusasshiyar Jam’iyyar NPN a Jamhuriyya ta Biyu Alhaji Isyaku Ibrahim ya shawarci ’yan siyasar kasar nan su guji bata juna, su tsaya su yi aiki tukuru don gina kasa. Alhaji Isyaku Ibrahim ya kuma yi kira ga masu rike da mukaman siyasa su rage habaici da soki-burutsu ga juna, su waiwayo don gina kasa, don ganin ta fita daga talauci da rashin tsaro zuwa ga kasa mai arziki da yalwa da zaman lafiya.

Alhaji Isyaku Ibrahim ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya kara da ce Najeriya tana cikin tsaka-mai-wuya saboda matsalar  rashin tsaro, inda masu rike da makamai suke cin karensu babu babbaka musamman masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce, ya dace masu mulki da sauran mabiya su dage domin ganin an samar da yanayin da kowa zai iya zama a ko’ina cikin lumana ba tare da tsaro ba.

Don ba a ci gaba sai da tsaro da fahimtar juna. Ya ce abin ban haushi ne yadda a koyaushe a kafafen watsa labarai na cikin gida da na waje suke ta yayata cewa ana ci gaba da yin garkuwa da mutane.

Ya shawarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hori ministocinsa su bar yawan magana,  su maida hankali wajen yin aiki don gina kasa da samar wa matasa aikin yi don shi ne babban abin damuwa ga kasar nan.

ADVERTISEMENT
Share