✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan siyasa ne ke iza matasa yin daba da shaye-shaye – Dokta Iguda

Wani Malami a Sashen Koyar da Aikin Jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano, Dokta Sanusi Iguda ya ce ’yan siyasa ne ummulhaba’isin kara iza…

Wani Malami a Sashen Koyar da Aikin Jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano, Dokta Sanusi Iguda ya ce ’yan siyasa ne ummulhaba’isin kara iza wutar shaye-shayen miyagun kwayoyi da harkar daba a tsakanin matasan kasar nan.

Malamin ya bayyana haka ne a wajen taron wayar da kai kan shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa da Kungiyar Wayar da kai game da Harkar Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi ta IFADE ta shirya.

Dokta Iguda ya ce yawancin ’yan siyasa sun dogara kacokan ne a kan matasa tun daga kan yakin neman zabe har zuwa lokacin yin zaben. “Idan kun duba yawancin ’yan siyasa sun dogara ne kan matasan da ke yi musu aiki wajen yakin neman zabe har zuwa cin zabe. Wadannda kuma suna sane da duk abubuwan da matasan ke yi da suka shafi maganganunsu da ayyukansu, suna yi ne sakamakon shaye-shayen miyagun kwayoyi. Wadansu ’yan siyasar ma har kudi suke ware wa matasa don yin shaye-shayen musamman don su bugu su aiwatar musu da abin da suke so,” inji shi.

Malamin ya nuna takaici kan yadda aka san Jihar Kano da dabbaka abubuwan da suka shafi addini, amma sai ga shi an wayi gari ita ce jihar da ke kan gaba ta fuskar tu’ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan.

Tun farko a jawabinsa na bude taron mai taken ‘Rawar da Kafafen Watsa Labarai Za su Taka Kan Yaki da Miyagun Kwayoyi’, Shugaban Kungiyar ta kasa, Kwamared Mukhtar Iliya ya ce  kafafen labarai suna da tasiri mai girman gaske ga rayuwar jama’a.

Ya ce “Tasirin da kafafen wasta labarai suke da shi wajen jama’a ba zai misaltu ba, domin mutane suna kwaikwayon abubuwa da dama da suka ji ko suka gani a kafafen watsa labarai, don haka akwai rawar da kafafen labaran ya kamata su taka wajen yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi ta hanyar bullo da shirye-shirye managarta da za su  fadakar kan haka.”

Da yake karin haske, Manajan Daraktan Gidan Rediyon Jihar Kano, Malam Umar Sa’id Tudun Wada ya ce kafafen watsa labarai suna iya kokarinsu wajen gabatar da shirye-shirye a kan yaki da miyagun kwayoyi, sai dai suna da tarnaki game da yadda Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC) ta iyakance kan yawan shirye-shiryen da za su gudanar.

“Hukumar da ke kula damu ta sa mana doka cewa ba za mu gudanar da shirye-shiryen da suka shafi addini da kyautata da’a da suka wuce kashi biyar na gaba dayan shirye-shiryenmu ba. Hakan ya zame mana tarnaki, sai dai duk da haka muna iya kokarinmu wajen wayar da kai a kan wananan mummunar dabi’a ta shaye-shaye,” inji shi.