✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan siyasa ne ke rura wutar rikici -Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce Najeriya ba ta fuskantar kowane irin barazana game da zaman lafiya a tsakanin addinai da kabilunta…

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce Najeriya ba ta fuskantar kowane irin barazana game da zaman lafiya a tsakanin addinai da kabilunta daba-daban kamar yadda wasu ke hasashe.
Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a wuri taron hadin kan kasa da wa’azi da kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa ta yi gudanar a Legas, inda ya ce ’yan siyasa ne kawai ke yin kalamai marasa dadi da suke kawo wasu ’yan rudani a nan da can, inda irin wadannan kalamai suke jawo a ga kamar kasar ta kama da wuta.
Sarkin Musulmi ya ce idan aka kwatanta yawan’yan siyasa da sauran jama’ar kasa za a tarar ’yan siyasa su ne kalilan domin yawancin talakawa suna zaune lafiya da junansu kuma suna fafutikar dan abin da za su ci ne ba ruwansu da harkokin siyasa kuma duk ko daga ina ’yan siyasar Najeriya suka fito sai ka tarar halinsu daya ne.
Sai ya yi kira ga ’yan siyasa su rage irin kalamansu na tunzura jama’a su rika sa wasu su dauka kasar ba ta zaune lafiya ko kamar yanzu kasar za ta kama da wuta.
Ya yaba wa kungiyar Izala kan shirya wannan taro, inda ya ce yin haka zai rika tunatar da al’umma cewa kowa na da hakki a kan dan uwansa.
A jawabi Mataimakin Shugaban kasa Muhammad Namadi Sambo ya ce zaman lafiya shi ne kashin bayan samar da ci gaba ga kowace al’umma. Ya ce duk yadda shugabanni suka so su samar da ci gaba ga jama’ar da suke wa jagoranci, muddin ba zaman lafiya zai yi wahala wannan al’umma ta samu ci gaban da take bukata.
Ya yaba wa kungiyar Izala kan shirya taron da kuma wa’azi domin fadakar da Musulmi da mabiya sauran addinai muhimmancin hadin kan kasa da zama lafiya, ya ce kowane dan kasa na da gudumawar da zai ba da wajen samar da zaman lafiya cikin kasar nan.
Gwamnan Jihar Osun, Injiniya Rauf Aregbesola a kasidar da ya gabatar a taron cewa ya yi daya daga cikin hanyoyin da ake bi domin samun dauwamammen zaman lafiya su ne hakuri da juna musammam a tsakanin mabiya addinai dabn-daban da kabilu. Ya ce, “Muddin muka mutunta addinin juna, babu abin da zai haifar da kowane irin rudani a cikin al’umma.”
Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau a jawabinsa ya yi wa shugabanni nasiha ne su yi adalci inda ya ce shi kadai ne zai kai su ga cimma burinsu duniya da Lahira.
Da ya tabo batun kashe malamai, inda ya ce duk al’ummar da ta shiga kashe malamanta tana cikin hadari da fuskantar bala’i.
Taron na yini uku ya samu halarta mutane daga kasashen Afirka bakwai da suka hada da Najeriya da Nijar da Bukina Faso da Kwaddibuwa da Ghana da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Benin.