✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan siyasa sun gurbata malaman addini – Bishop Markus Dogo

Bishop Markus Madugu Dogo shi ne Shugaban Darikar Anglican na Kafanchan (Kudancin Kaduna). Shugaban ya shahara a tsakankanin mabiya addini musamman kan yunkurinsa na ganin…

Bishop Markus Madugu Dogo shi ne Shugaban Darikar Anglican na Kafanchan (Kudancin Kaduna). Shugaban ya shahara a tsakankanin mabiya addini musamman kan yunkurinsa na ganin an daina zubar da jini a sassan Kudancin Kaduna tare da samun kyakkyawan fahimtar juna tsakanin musulmi da kiristoci.

Wace gudunmuwa malaman addini za su bayar wajen zaman lafiya?

A gaskiya malaman addini na da gagarumar gudummawa da za su bayar wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a cikin al’umma. Amma da farko tukuna ya kamata mu san cewa malami fa shi ne wanda yake da zurfin ilmi da kwarewa a kan wata fanni ko wasu fannoni. Kuma shugabanci da ilmi wasu abubuwa ne da ke tafiya tare don ba a raba su domin duk mutumin da ba shi da ilmi ba zai iya jagorantar mutane zuwa ga daidai ba. Manyan matsalolin da ke addabarmu a Najeriya da suka hada da tsattsauran ra’ayin addini da yin garkuwa da mutane da kashe-kashe duk suna da alaka da karancin sani.

Yawancinmu a nan kasar imma dai musulmi ko kirista, amma mu na da matsalar karancin sanin addinanmu. Wannan dalilin ne yasa mu ke fassara addinin a baibai ta yadda a karshe shike kyankyashe gurbatattun al’umma a cikinmu mai cike da son tashin hankali.

Shi karantarwar addini ba ya tsaya ga bautar Allah ne kadai ba, ya hada har da yadda za ka yi mu’amala da jama’a. Idan ka dauki misalin addini kiristanci, cikin dokokin nan guda goma da ya zo a cikin baibul ai guda hudu ne kawai suka yi magana kan alakarka da Ubangiji amma sauran guda shidan suna magana ne kan alakarmu da sauran jama’a.

Ko kana aikin samar da zaman lafiya tare da kungiyoyi masu zaman kan su?

Babu wata kungiya dai takamaimai da ke aikin wanzar da zaman lafiya da nake aiki da su, amma dai ina gudanar da wasu ayyukan da suka shafi hakan. Na halarci kasashe da dama kan wannan dalilin. Misali na je wasu majami’u a garuruwa da dama a kasar Amurka. Na je Coci mafi girma a duniya da ke kasar Korea wacce ke daukan masu ibada mutum miliyan daya da dubu dari hudu a kowace ranar lahadi, sannan a bara na je kasar Isra’ila don nazarin yadda Yahudawa ke tafiyar da yanayin zaman lafiya tsakaninsu da sauran jama’a. Na gabatar da mukala a Washington DC a wajen taro sannan a bara ma na sake gabatar da wata mukala a Michigan ta kasar Amurka inda aka tattaro malaman addinin musulunci da na kiristanci daga kasashen duniya. A can ne na hadu da wani malami Musulmi dan kasar Turkiyya wanda nake sa ran gayyato shi watarana tare da wani daga cikin malaman addini kirista zuwa nan Kafanchan saboda irin usulubin wa’azinsu na hadin kai da zaman lafiya da muke da bukatar irinsa a kudancin Kaduna da Najeriya baki daya.

Ana zargin cewa da yawa daga cikin malaman addini ‘yan siyasa sun gurbata su?

Babu tantama wannan maganar haka take! Idan ni ba ni daga cikin irinsu ai akwai da dama a ciki. Ni a fahimtata, daga cikin nauyin da ya hau kaina a matsayina na shugaban addini guda biyu, littafin baibul ya karantar dani girmama shugabanni kuma daidai gwargwado ina girmamasu. Abu na biyu kuma bayan girmamawar shi ne fada wa mutum gaskiya ko wane ne shi. Yanzu matsalar da ake ciki ita ce malamai nawa ne za su iya tsayawa a gaban masu mulki su fada musu gaskiya? Idan har dan siyasa zai kawo min ziyara sannan ya dauki Naira miliyan daya ya ba ni na kuma karba na soke, ta yaya zan iya fuskantarsa in fada masa gaskiya?

To idan muka koma shekarar 2011 lokacin rikicin bayan zabe da aka yi, daidai lokacin ne aka turo ni Kafanchan saboda tunanin irin gudummawar da zan iya bayarwa. Abu guda daya da na lura da shi shi ne tun daga lokacin har zuwa yau din nan babu wani mutum ko guda daya da ya shiga hannu a sanadiyyar rikicin har zuwa yau da sauran rikice-rikice su ka biyo baya tare da shan alwashin da gwamnati ta yi na kamo masu laifi da kuma hukunta su.

Bayan zuwan wannan gwamnatin na APC, Gwamnan Jihar Kaduna ya yi ta rantse-rantse a wurare daban-dabam kan sai ya kamo kuma ya hukunta duk wanda aka kama da laifin tada zaune tsaye.  Abin takaicin shine har yau babu wanda ya shigo hannu.

Game da rikicin manoma da makiyaya sai in ce shi ma ba ba za ka taba cire hannun ‘yan siyasa a ciki ba. Ni fa abin da na yi imani da shi shi ne duk wanda ya yi ba daidai ba a hukunta shi kawai. Me zai sa za a rika kyale masu laifi suna tafiya ba tare da hukunci ba? Idan fa har ba za a rika hukunta masu laifi don zama darasi ga ‘yan baya ba to kullum zai ci gaba ne da aikatawa.

Idan har gwamnati za ta rika sanya son rai a cikin lamarin to ba ranar da za a fita daga wannan matsalar.

Yanzu da aka fara buga gangar siyasar 2019; wanne kira kake da shi zuwa ga matasan Najeriya?

Babu shakka matasa suke dauke da kaso mafi yawa a kasar nan. Don haka shawarata ga matasa ita ce idan har sun gamsu da nagarta da ayyukan wanda suka zaba shi ke nan sai su sake zabansa karo na biyu amma idan ba ka gamsu da salon mulkinsa ba sai ka yi waje da shi tunda babu wani ma’asumi a cikinsu.

Tunda ko haka ne babbar shawarata ita ce ta hanyar kuri’a ne kawai za ka iya huce fushinka ba wai ta hanyar tarzoma ba, don haka matasa su guji tashin hankali da daukar doka a hannu lokacin zabe a duk irin matsayin da suka tsinci kansu. Abin da nake fada wa mutane ke nan a coci cewa kowa na da ikon zaban duk dan takarar da ya yi masa kamar yadda doka ta ba shi, amma idan mutum yayi mummumar zabi to sakamakon zai dawo mishi ne, shi da jama’arsa.

Yanzu lokaci ya wuce da wani dan siyasa zai zo ya rude ku da Naira dubu biyar ku je kuna ganganci da rayukanku.

A karshe me za ka ce kan mutanen da ke amfani da addini wajen haddasa fitina ko ba da kariya ga ‘yan uwansu idan sun haddasa fitina?

Wadannam dakikai ne jahilai marasa hankali. Wadannan ba su ma san karantarwar addinansu ba. Ta daya mutum zai taimaki mai haddasa fitina a cikin al’umma ko ya ba shi kariya ya rika boye shi kada a hukunta shi don kawai addininsu daya?

Yanzu idan wani ya je ya aikata ba daidai ba, wanne addinin ne ya umurce shi da ya aikata haka? To don me za ka rika goyon bayan shi? Wannan yana gwada irin tsattsauran ra’ayin addini ne  kawai. Ba ga kiristoci ba, ba ga musulmi ba kowa na yi saboda gurbata mutane da wani irin karantarwa. Duk mai aikata haka ya san baya taimakon addinin Allah kuma baya taimakon al’ummarsa sannan bai yiwa kansa adalci ba.

A karshe zan sake nanatawa, dukkanin abin da mutum ya aikata akwai ranar kin dillanci, ranar da kowa zai tsaya a gaban Allah domin ya yi bayani.