✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan ta’adda na amfani da shafukan zumunta don samun mambobi – Pantami

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet, Dokta Isa Ali Pantami, ya yi ikirarin cewa ’yan ta’adda na amfani da shafukan sada zumunta na zamani domin…

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Intanet, Dokta Isa Ali Pantami, ya yi ikirarin cewa ’yan ta’adda na amfani da shafukan sada zumunta na zamani domin daukar sababbin mambobi da kuma tsara yadda za su kai hare-hare.

Ministan yana wadannan kalamai ne a wurin taro kan yadda za a dakile ta’addanci da aka gudanar a Abuja, inda ya ce akwai bukatar samar da hanyoyin hikima wajen dakile ta’addanci da kuma hana faruwarsa baki daya.

“A fili yake cewa ’yan ta’adda na amfani da shafuffukan sada zumunta da hanyar boye yadda ake sadarwa wajen watsa farfaganda da kuma samun sababbin mambobi,” in ji Ministan.

Ya yi kira ga jami’an tsaro su yi amfani da fasaha wurin shawo kan ’yan ta’adda da kuma dakile hare-haren da suke kai wa jama’a.