Da Dumi Dumi

’Yan ta’adda: Yadda mutanen Zamfara ke tururuwar neman maganin bindiga

Jerin gwanon masu neman maganin bindiga a qauyen Tsauni da ke ‘Yankuzo a yankin Tsafe Jihar Zamfara. Hoto daga Ibrahim Sheme
Jerin gwanon masu neman maganin bindiga a qauyen Tsauni da ke ‘Yankuzo a yankin Tsafe Jihar Zamfara. Hoto daga Ibrahim Sheme

Wani mutumin Katsina ya rasa ransa wajen gwajin maganin

Daruruwan mutane daga yankunan Jihar Zamfara da makwabciyarta Jihar Katsina suna ta yin tururuwa zuwa neman maganin bindiga a wani mataki na kare kansu daga hare-haren da ’yan bindiga suke kai musu ba kakkautawa don yi musu fashi ko kuma garkuwa da su.

Aminiya ta gano cewa daruruwan mutane daga sassan Jihar Zamfara suna ta tururuwa zuwa kauyen Tsauni da ke Gundumar ’Yankuzo a Karamar Hukumar Tsafe da ke jihar ta Zamfara domin shan maganin bindigar da ake sayarwa a wurin.

Wani matashi ne ake ikirarin yana ba da maganin bindigar kuma mutanen da dama da suke karbar maganin suna cewa lamarin matashin lamari ne mai ban mamaki da suke jingina lamarinsa da aljanu.

Mutane da dama a yankin sun yarda cewa shan maganin bindigar zai kare su daga harbin bindigar abokan gaba. Wannan lamari yana zuwa ne bayan da Jihar Zamfara ta zama wani fage na zama cikin fargabar harin ’yan bindiga wadanda suke matukar barna a yankunan karkarar jihar.

ADVERTISEMENT

Jama’ar da suke tururuwar zuwa kauyen na Tsauni, wadanda kuma suka zanta da wakilinmu sun ce shan maganin bindigar shi ne zabin da ya rage masu a yanzu son haka za su yi bakin karfinsu wajen kare kansu.

“Da zarar ka zo nan to za a ba ka wata ’yar karamar laya da kofin ruwa domin ka hadiye, bayan ka hadiye ne za ka ba da Naira 200 sannan za a yi ma ruwan alburusai domin gwada ingancin maganin. Babu wanda ake bari ya tafi da ’yar karamar layar zuwa gidansa. Duk wanda aka ba shi layar to za a fada masa cewa ya hadiye ta nan take,” Inji wani mazaunin yankin mai suna Bala Hassan.

Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa, da farko akan rataye layar ce a kan itaciya sannan a umarci masu rike da bindagogi su yi wa bishiyar ruwan harsasai kuma harsasan ba zu kai ga bishiyar ba. Wannan ana yin sa ne domin a gwada wa mutane ingancin maganin.

“Mutane da dama sun yi imani da ingancin maganin kuma ta kai ga idan aka san ka hadiye layar za a yi ta dirka maka bindiga ba tare da harsashi ya huda ka ba. Mutanenmu sun fahimci cewa su ma ’yan bindigar duk da suna da makamai wadanda suka fi namu, suma suna shan maganin bindiga, don haka ba za mu taba bari su tsere mana ta fuskar kare kai ba,” inji wani mazaunin yankin mai suna Danmalam Sani.

To sai dai wadansu muttane da wakilinmu ya zanta da su, wadanda kuma ba su son a ambaci sunayensu, sun ce su sam ba su yi imani da wani abu da zai kare mutum daga harbin bindiga ba, don haka kada mutane su yi imani da shi.

“Ai Malam da zarar an harba bindiga to babu abin da zai hana ta fitar da harsashi ya kuma doki abin da aka hara da shi. Masu shan maganin bindigar sun yi imani da shi kwarai don haka babu abin da zai same su. Ina tunanin maganin bindiga ya fi karfin dabi’a irin ta dan Adam. Don haka wani ya ce wai idan harbe shi harsashi ba zai huda shi ba, to gaskiya sai dai shi idan wani abin mai rai ba ne ko ba dan Adam ba,” inji shi.

Shi kuwa wani mazaunin yankin mai suna Lawali Hamisu ya alakanta tururuwar da jamaa suke yi zuwa wurin shan maganin bindigar da gazawar gwamnati da jamian tsaro wurin kare rayukan jamaa da dukiyoyinsu.

“Me zai sa mutane su damu da wani maganin bindiga idan jami’an tsaro suna aikinsu? Shin maganin bindigar shi ne kadai zabin da ya rage wa jama’a wurin kare kansu? Shin har zuwa yaushe mutanen za su dogara a kan asirin bindiga? Wadannan tambayoyi ne da suke bukatar amsa,” inji shi.

Baya ga shan maganin bindiga jama’a kuma na ta gasar mallakar kananan bindigogin da ake kira “Mai Fulogi” a yankin. Wadansu wadanda suka yi magana da Aminiya sun ce farashin wannan bindiga ya fara ne daga Naira 5,000 zuwa 6000.

Ita dai wannan bindiga tana amfani ne da filogi na injin babur a matsayin harsashi, don haka ake kiranta “mai fulugo ko mai fulogi” kuma jama’a da dama a yankin suna mallakarta ce don kare kansu.

Idan ka shiga yankunan karkarar Jihar Zamfara zai yi wahala ka iya bambance tsakanin ’yan banga da sauran jamaar gari saboda yadda wannan bindiga ta yawaita a hannun jama’a.

“Ina daukar bindiga ta zuwa gona, kasuwa da kuma duk wurin da zan tafi don kare kaina, idan ba ka dauke da wani makami na kare kai a wannan yanki namu to kana cikin matsala,” inji wani mai bindiga.

To sai dai akwai masu ganin cewa yawaitar kananan makamai a hannun jama’a ba alheri ba ne saboda makaman za su iya fadawa hannun ’yan taadda kuma su yi amfani da su wajen aikata ta’addanci.

Aminiya ta samu labarin cewa wani mutumin Jihar Katsina, mai suna Abu Sadara, ya rasa ransa a lokacin da aka harbe shi da bindiga don gwada aikin layar da aka ba shi a matsayin kariya daga harbin bindiga a kauyen Kwari da ke yankin Farafara a Karamar Hukumar Jibiya, yayin da wani mai suna Mani Dogo-Dogo yake kwance rai kwakwai mutu kwakwai sakamakon raunin da ya samu wajen gwajin maganin harbin bindigar. Marigayin da Dogo-Dogo da wadansu mutum biyu sun tafi har Kankara ne don amso maganin bindigar.

Mazauna yankunan karkara a sassan jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da suka yi iyaka da Dajin Rugu dai suna fama da ayyukan ta’asa na masu garkuwa da mutane da masu satar shanu lamarin da yake sanya jama’a zaman cikin tsoro da firgiji, inda suke tafka asara sakamakon karuwar ayyukan ’yan bindigar. Kananan hukumomin da suka fi kusa da bakin dajin nan na Rugu ne da ke zama mafaka ga masu garkuwa da mutanen da ’yan bindiga ne suka fi haduwa da farmaki a kai a kai daga ’yan bindigar, wadanda bayan sun yi ta’asarsu sai su fada cikin dajin su buya.

A wannan yanki ne aka sacetare da yin garkuwa da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Alaramma Ahmad Sulaiman wanda aka sako shi a ranar Larabar makon jiya bayan ya shafe kusan mako biyu a hannun masu garkuwa da mutane da suka kama shi tare da mutum biyar.

Ko a makon jiya shekaranjiya mutanen yankin sun fatattki wadansu da suka kai musu hari ta hanyar amfani da dabarun kare kai. A lokacin harin an raunata ’yan bindiga da dama yayin da aka kama wadansu aka mika wa jami’an tsaro. Sai dai mutanen yankin suna kuka kan yadda jami’an tsaro suke sake ’yan bindigar bayan ’yan kwanaki kadan da kama su.

Malam Sani Sa’adu wani masanin halayyar dan Adam kuma babban mai bayar da shawarwari da lallashi a Sashin Harkokin Dalibai na Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa da ke Katsina ya ce, tururuwar da jama’a suke yi don neman maganin bindigar na nuna akwai bukatar masu ruwa-da-tsaki su dauki matakin dakile abin wanda zai yiilla ga tunanin jama’a. Ya ce akwai bukatar a kara fadakar da jama’a su guji irin wannan abu, domin ya saba wa hankali da tunani kuma ba shi ne mafita ba

“Wannan barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar shi kansa mutumin, kuma ya wajaba hukumomi su shigo cikin lamarain, domin daga abin da na lura, yadda ake tururuwa ana zuwa neman maganin bindigar abin ya wuce hankali,” inji shi.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya