✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan ta’addan Zamfara mece ce ribarku?

Assalamu alaikum Edita, don Allah ka ba ni dama in yi kira ga ‘yan ta’addan Zamfara wadanda suke kashe bayin Allah da ba suji ba,…

Assalamu alaikum Edita, don Allah ka ba ni dama in yi kira ga ‘yan ta’addan Zamfara wadanda suke kashe bayin Allah da ba suji ba, ba su gani ba. A gaskiya masu kisan nan ba ku da imani ko kadan, ko kun san mata nawa kuka raba da mazansu? Ko kusan adadin yaran da kuka mai da su marayu? Kada ku manta wanda ku kashe inda sukaje kuma sai kun je. Ina tunanin ba ku manta ba cewa, Allah Ya tanadi wuta da Aljanna? Muna rokon Allah Ya yi mana maganinku don alfarmar Annabi Muhammad (SAW).

Daga Nasir Idris Tarai 07033901873.

Mun amince da tsarin ’yar Tinke a Katsina

Assalmu alaikum Edita. Mu al’ummar Jihar Katsina mun amince da tsarin Jam’iyyar APC na zaben ’yar Tinke a Jihar a Katsina (Direct Primaries) ganin haka yana hana cin hanci da rashawa da ya yi wa zaben edco/delegate kaka gida wajen kawo cikas ga sha’anin siyasar kasar nan da kuma kawo bara-gurbin shugabanni da wakilai a madafun iko na kasar nan.

Daga Auwal Abubakar dandagoro 08038414144.

Jinjina ga Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Edo

Assalamu alaikum Edita. Ina muku fatan alheri da fatan Allah Ya saka muku da albarka amin. Ina son ku ba ni dama in gode wa Kwamishinan ’Yan sandar Jihar Edo Mista Johnson, kan kudirin kwato jaririyar da talauci ya sa uwarta ta sayar a garin Anacha, Allah Ya ba shi iko da basirar wannan aiki, inda hali ku aiko min lambar wayar mijin matar da ta sai da yaron.

Daga  Rabaran Abiru Solomon (08104757646).

Jinjina ga Kwankwaso

Salam Edita. Ka ba ni dama in yi jinjina ga Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa raya Sunnar Annabi Muhammad (SAW) ta aiwatar da auren zawarawa da ya yi. Ya Allah Ka saka masa da Aljanna amin, ka biya masa bukatunsa na alheri amin. Kuma Allah Ka sa sauran shugabanni su yi koyi da shi amin kuma muna fatan alheri. Muna yi masa addu’ar Allah Ya kare shi, Ya yi masa jagora wajen tafiyar da harkokin mulkin kasar nan cikin nasara.

Daga Safeenat Is’hak 08122800227.

Masu canjin sheka sun sayar da rago ne suka sayo biri

Assalamu alaikum Edita. Ka ba ni dama domin in shaida wa ’yan siyasar da suka canja sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP. A gaskiya wadannan ’yan siyasa sun sayar da rago ne suka sayo biri. Don haka tsugune ba ta kare musu ba domin Jam’iyyar PDP takenta na shegiyar uwa mai kashe ’ya’yanta yana nan. Kuma nan da lokaci kadan za mu gan su a rana.

Daga Alhaji Adamu Shuwa Damboa, Mpape, Bwari Abuja. 08089532467, 08055945695

Fom din takarar APC ya yi tsada ga talakan Najeriya

Assalamu alaikum Edita, ka ba ni da in yi kira ga uwar Jam’iyyar APC ta kasa ta duba ta ga halin da talakawa suke ciki na rashin kudi, ta sassauta kudin fom din takara ta yadda talaka zai samu damar shiga takarar. Idan ba haka ba ba za a samu shugabanni nagari ba wadanda za su iya kawo canji mai amfani ba. Allah Ya zaba mana shugabanni nagari masu tausayinmu ba masu samu hawaye da idonmu ba.

Daga Abdullahi Dibo Jama’are 08132428869.

Muna bayan Shekarau a ko’ina

Assalamu alaikum Edita, Aminiya don Allah ku isar min da sakona zuwa ga Mallam Ibrahim Shekarau mu ma mun bi mun bar Jam’iyyar PDP mun koma APC jam’iyyar adalci.

Daga Shamsu Mai Kadara Kano 08033532155

Kyautata albashin ma’aikatan jihohi zai inganta tsaro

Salam  AMINIYA don Allah Baba Buhari ka taimaka wa ma’aikatan jihohi su amfana da sabon albashi. Wannan zai taimaka ga kyautata tsaro da ilimi da noma da arzikin jama’ar Najeriya.  A shiyyar Arewa babu kamfanoni yayin da har ’yan kasuwa suna amfana da ingantaccen albashi daga ma’aikata.

Daga Iro Katsina 07069524577

Jinjina ga Sakataren UBE Lawal Buhari

Assalamu alaikum Edita. Ka ba ni fili in yi godiya ga Babban Sakataren Hukumar Ilimi Bai-daya ta Jihar katsina Lawal Daura kan inganta ilimin da yake yi a fadin jiha da yadda yake daukar malamai da yadda yake aiwatar da sababbin dabarun koyarwa na zamani da yadda yake tura malamai karo karatu gida da waje da yadda ya hada kai da Bashir Yashe na NTI ta Jihar Katsina wajen shirya wa malamai taron bita da sanin makamar aiki da biyan albashi a kan kari da karin girma ga wanda ya cancanta da ba da kayan aikin koyarwa isassu, Allah Ya kara girma.

Daga Amiru Bakori, Sashen Ilimi na karamar Hukumar danja, 08084213547.

 ‘Yan siyasar Najeriya ku yi koyi da mazan jiya 

Assalamu alaikum Edita. Dimukuradiyya a Najeriya, da a ce ’yan siyasan yanzu za su gaji halin mazan jiya, da ’yan Najeriya sun yi alfahari da su. Sai in kun tashi neman zabe, kuka sa kasa ta lalace wasu suka lalata ta, PDP ke ce siyasarmu lokacin baya mun dauke ki uwa uba ashe mugun iri ce, kin tara mutanen da muke gani da kima a gurinmu.

Daga Jada 07034542318.

Jinjina ga Ado Sale Kankiya 

Assalamu alaikum Editan wannan jarida tamu mai albarka. Ina so ka ba ni dama in yaba wa fitaccen dan jaridar nan wato Ado Sale Kankiya da wannan jarida ta AMINIYA bisa rubutun da ya yi a wannan jarida ta ranar 10 ga Augusta mai taken “SIYASA KASUWAR BUkATA”. Hakika wannan rubutu nasa ya haska mana cewa wadannan ’yan siyasa biyu da ya yi rubutu a kansu ba za su iya zama a inuwa daya ba. Kuma sai ga shi a ranar 4 ga Satumba 2018, hakan ta tabbata, hakika mu talakawa lokaci ya yi da ya kamata mu fahimci ’yan siyasa masu yi don aljihunsu da masu yi don talaka.

Daga Magaji Aminu Biglucky Rijiyar Lemo, Jihar Kano.

 Fatan alheri ga Baba Balarabe Musa 

Salam Edita. Fatan alheri gare ka da dukan ma’aikatanka, da fatan kuma za ka ba ni fili a wannan jarida mai farin jini domin na mika ban-gajiya tare da fatan alheri ga dan kishin kasar nan, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa bisa ajiye harkokin siyasa da ya yi. Da fatan cikawa da imani, amin.

A. Rufai Kachako, Kano 08086220921

Kira ga shugabannin bankuna 

Salam Edita,  ina so in yi kira ga bankuna a kan su yi wa Allah su rika zuba kananan kudi a cikin ATM kamar Naira dari biyu da dari daya da Naira hamsin kai harma zuwa Naira biyar idan dai ana so talaka ya samu saukin sarrafa kudade.

Daga Jamilu M. Adam 07037278401

Addu’ar samun nasara ga Baba Buhari

Salam Editan Aminiya. Muna yi wa Baba Buhari addu’a dare da rana Allah Ya ba shi sa’a da nasara. Mu Sakkwatawa muna tare da kai insha Allah Najeriya sai Baba Buhari.

Daga Abubakar Harande Shagari 08080256772.

Kira ga Gwamnan Jihar Kano  

Assalamu alaikum Edita. Ina son ka ba ni dama domin in yi kira ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje,  ya taimaka a yashe mana dam din Thomas domin a gaskiya dam din ya cike ga shi dam ne mai albarka sosai wanda ake noman rani sosai kamar su albasa, atarugu, alkama, shinkafa, tumatir da sauransu. Ya Mai girma Gwamna idan aka yashe shi to jama’a za su kara samun aikin yi sosai damin yadda Shugaban kasar nan ya sa jama’a suka koma noma.

Daga M Lawal Maihula Kunya O8033992882.

Tambaya ga gwamnoni da ‘yan majalisa na APC

Assalamu alaikum Edita. Ina son ka ba ni dama domin in yi tambaya ga gwamnoni da ’yan majalisa na Jam’iyyar APC, sanin kowa ne a lokacin kamfen din shekarar 2015 duk inda dan takarar Gwamna ko dan Majalisar Tarayya ya je abin da suk ce wa talaka shi ne, ku ba mu goyon baya domin mu karbo mulkin kasar nan  daga hannun wadanda suka sace kudin da za a yi wa talakawa aiki da su kuma sai  kun yi APC sak, don sai Shugaban kasa  ya samu rinjaye a majalisa  zai ji dadin tafiyar  da mulkinsa.  Tambayata a nan ita ce an kori azzaluman gwamnoni da ’yan majalisa. Yanzu adalai ne aka zaba? Shugaban kasa yana jin dadinsu? Ina sauraron amsa.

Daga Hadi Tsohon Sarki, Daura  08164205067- 08136433609.