✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan takarar APC 75 sun sayi fom ta barauniyar hanya – Mathewe Achigbe

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kuros Riba, Mista Matthew Achigbe ya fadi a Kalaba cewa, kimanin ’yan takara 75 ne suka sayi fom ba tare…

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kuros Riba, Mista Matthew Achigbe ya fadi a Kalaba cewa, kimanin ’yan takara 75 ne suka sayi fom ba tare da sun cika sharudda ba, wato sun saya ne ta baraumiyar hanya.

Wannan kuwa na da nasaba da cewa Jam’iyyar APC a Jihar Kuros Riba tana fama da rikicin cikin-gida kan shugabancin jam’iyyar, a tsakanin bangaren Ministan Al’amuran Neja Delta, Fasto Usani Usani da na shugaban shiyyar Kudu maso Kudu, Mista Hillary Ettah.

Kuma kamar yadda wakilinmu ya kalato, akwai matsala a bangaren Shugaba Godwin John Etim da na Matthew Achigbe, duk da kasancewa wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta warware takaddamar.

Sakataten Jam’iyyar, Mista Francis Ekpenyong a ganawarsa da manema labarai ya nanata cewa shi ne halattaccen Sakataren Jam’iyyar da Babbar Kotun Abuja ta yanke hukunci a kai.