Da Dumi Dumi

’Yan takarar Gwamnan Nasarawa 11 a APC sun turo mota ta bar su da kura

Abdullahi Sule, Gwamnan Jihar Nasarawa
Abdullahi Sule, Gwamnan Jihar Nasarawa

Bayan sanar da fara sayar da takardun neman tsayawa takara a zaben Gwamnan Jihar Nasarawa da ya gabata a  karkashin Jam’iyyar APC,  wadansu jiga-jigan ’ya’yan jam’iyyar sun nuna sha’awar  fitowa takarar. Duk da tsuga kudin sayen fom din takara a Jam’iyyar APC i a zaben na bana inda kowane dan takara takarda ya sayi fom din a kan Naira miliyan 20, duk da haka jam’iyyar ce ta fito da ’yan takarar kujerar Gwamnan mafi yawa a zaben daya gabata a tarihin zabe a kasar nan baki daya. Jam’iyyar APC a Nasarawa na da ’yan takara da suka fafata a zaben fid da gwani har su 11 inda a karshe Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule ya samu nasara.

Wakilinmu ya gano cewa bayan kammala zabe a jihar al’ummar jihar sun zuba ido kan za a nada wadansu daga cikin wadanda suka fafata a takarar, a  manyan mukamai a jihar da kuma a Gwamnatin Tarayya. ’Yan takarar Jam’iyyar APC 11 da suka nemi kujerar Gwamnan da ake yi musu lakabi da The Eleben Horse Men sun ki canja sheka zuwa wata jam’iyya duk da sha-kaye a zaben fid da gwanin, bisa sa ran a saka wa hakuri da goyon baya da suka nuna wa jam’iyyarsu ta APC sun taimaka har ta kai ga lashe kusan kujerun da ta tsaya takara a jihar. A zantawarsa da wakilinmu daya daga cikin ’yan takarar 11 da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce lallai sun turo mota ta tafi ta bar su da kura.

Ya ce, “Kamar yadda ka sani ni ma daya ne daga cikin  ’yan takarar Gwamna na jam’iyyarmu ta APC. Ni dai kawai abin da zan bayyana maka a takaice shi ne gaskiya ba a yi mana adalci ba, ya kamata a saka mana, don kai dan jarida ne ba sai na bayyana maka irin gwagwarmaya da dukkanmu muka yi bayan mun fadi zaben fid da gwani ba. An ba mu hakuri kan mu kasance a cikin jam’iyyar mu yi mata aiki tare da alkawarin za a saka mana a karshe. Amma har yanzu kamar yadda ka sani babu wani daga cikin mu 11 da ya samu wani mukami daga gwamnatin jihar nan ko ta tarayya, ga shi kuma an riga an nada muhimman mukaman da suka hada da na Sakataren Gwamnatin Jiha da na minista daga jihar nan da sauransu,” inji shi.

Share