✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yana da kyau mata su shiga siyasa – Safiya Sallari

Hajiya Safiya Aliyu Sallari Darakta ce a Ma’aikatar Ciniki da Kasuwanci ta Jihar Kano. Kuma fitacciyar ’yar siyasa ce a Jam’iyyar APC, ta taba zama…

Hajiya Safiya Aliyu Sallari Darakta ce a Ma’aikatar Ciniki da Kasuwanci ta Jihar Kano. Kuma fitacciyar ’yar siyasa ce a Jam’iyyar APC, ta taba zama mashawarciyar Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau kan Al’amuran Mata. A tattanawarta da Aminiya ta ce akwai bukatar mata su fito a dama da su a harkokin siyasa da sauran batutuwa:

 

Tarihin rayuwata:

An haife ni a Jihar Kano. Na yi karatun firamare a Makarantar Firamaren Shahuci. Bayan na gama na tafi Makarantar Sakandaren Mata da ke Kabo. Bayan na kammala sai na yi difloma a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Jihar Kano. A daidai wannan lokaci ne kuma na yi aure. Bayan na yi aure sai na samu aiki a Hukumar Bayar da Ruwan sha (WRECA). Ina nan ina aiki sai na je na karo ilimi inda na samu Babbar Difloma.  Bayan na gama karatu na dawo aiki sai aka raba hukumar  gida biyu wato bangaren Water Board da kuma WRECA, sai na samu kaina a bangaren Water Board. Ina nan sai na samu aiki da gidan rediyon Jihar Kano, inda aka dauke ni a matsayin mai bayar da sanarwa. A wannan lokaci na yi shirye-shirye da suka hada da ‘Don Matasa’ da ‘Daga Masu Sauraronmu’ da ‘Wasa Kwakwalwa’ da ‘Girke-Girke’ da saurasnu. Kuma nakan yi tallace-tallace kamar na fulawa mai kwabo da na maganin sauro da sabulun Canoe da sauransu.

Wani lokaci sai aiki ya mayar da maigidana Bauchi, to da muka koma Bauchi na yi aiki a gidan talabijin na BATB, ina daga cikin mutanen da suka fara karanta labarai a gidan talabijin din bayan da aka bude shi. Bayan mun dawo Kano sai na koma aikina a Hukumar Ruwa. Muna nan a lokacin gwamnatin Kanar Dominic Oneya sai aka kulla wata yarjejniya da otel din Daula da wani otel din Links don haka sai aka dauke mu a matsayin ’yan Kano masu gudanar da hotel din don mu kula da dukiyar Kano. Wannan ne dalilin da ya sa na koma Ma’aikatar Ciniki da Kasuwanci.

Lokacin da wadanda aka shiga yarjejeniyar da su wato masu otel din Links, bayan mun fara aiki sai muka kula ana cin amanar gwamnatin Jihar Kano hakan ya sa muka nuna ba mu son aikinsu. Daga nan muka mika wa gwamnati rahotanmu a kan hotel din hakan ya sa gwamnati ta janye yarjejniyar inda suka kwashe kayansu daga Kano suka bar garin.

 

Shigata siyasa

To ni dai zan iya cewa siyasa ce ta haife ni domin tunda na taso na tarar mahaifina yana siyasa wato PRP. Zan iya cewa na fara siyasa sosai a lokacin da Malam Ibrahim Shekarau ya zama Gwamnan Kano a karkashin Jam’iyyar ANPP. Kasancewar mun yi aiki da shi a Daula Hotel lokacin yana Babban Sakatare a Ma’aikatar Ciniki. Muna nan muna gwagwarmaya har daga baya Malam Shekarau ya ba ni mukamin Mashawarciyarsa Kan Harkokin Mata

 

Yadda nake kallon tafiyar mata a siyasa

Bari na fara da yadda nake kallon siyasa gaba daya.  Ni ina daukar siyasa a matsayin akida ba don samun wani abin duniya ko don yin suna ba. Wanda shi ne abin da ya yi wuya yanzu, domin yawancin ’yan siyasa a yanzu ba siyasar akida suke yi ba, suna yi ne kawai don samun wata biyan bukata. Za ki yarda da ni idan kika ga yadda ’yan siyasa sukan bar jam’iyyarsu a lokacin da suka ga sun fadi zabe. Wanda kuma hakan ba daidai ba ne. Idan ka bar jam’iyyar to ai ka yi butulci domin idan ka duba babu abin da jam’iyyar nan ba ta yi maka ba. Ko kuma ki ga ’yan siyasa komai za a yi ba za su iya bugar kirji su yi amfani da kudin aljihunsu ba wai sai an ba su wani abu. Ita siyasa ’yar halal ce idan ka wahala mata to wata rana za ka more ta amma fa ba wai ka ce yanzu-yanzu za ka samu kudi a siyasa ba.

Haka kuma na yi imani da siyasar ubangida domin a ganina duk dan siyasar da ba ya da uban gida to ba siyasa yake yi ba, don haka Malam Shekarau shi ne uban gidana a siyasa. Ko Shugaban Kasa ne idan ba ya da uban gida a siyasa to akwai matsala. Hakan kuma ya sa na dora a kan ra’ayina musamman da na samu kaina a gidan siyasar Malam Ibrahim Shekarau domin ya tarbiyyantar da mu a kan siyasa don akida.

Idan na koma kan mata ’yan siyasa ba wani abu ba ne don mace ta shiga siyasa, bai taba addininta ba haka kuma aurenta. Idan mace za ta rike mutuncin kanta za ta iya yin siyasa ba tare da wata matsala ba. Don haka ma yanzu ya kai mutane sun fara karbar siyasar mata a Jihar Kano.

Wuri daya ne mata zan iya cewa ba su samu a siyasa ba shi ne cin zabe. Ni a ganina abu biyu ne ya jawo mata ba su samun damar tsayawa takara. Abu na farko yanayin al’adarmu da ba ta bayar da dama ga mata su yi shugabanci ba, amma a yanzu al’umma sun fara karbar lamarin, domin a yanzu malamai suna ta wa’azi a kan cewa mata za su iya yin wakilci. Na biyu kuma abin da ke hana mata samun takara shi ne yadda mata ba su shigowa a yi gwagwarya da su a siyasance sai dai kawai idan zabe ya gabato su taho daga Abuja su zo su sayi fom don yin takara. Ba zai yiwu a ce rana daya don kawai mace tana da kudi ta fito ta ce ta tsaya takara tana raba wa mutane Naira dari bibbiyu sannan ta yi tsammanin za a zabe ta ba. Mutane fa yanzu sun waye.

A ganina a yanzu ana damawa da mata a siyasa tunda ana ba su mukamai a gwamnati. Ki duba gwamnatin Malam Shkearau ya bayar da mukamai da yawa ga mata haka Gwamna Abudllahi Ganduje shi ma ya bayar da manyan mukamai ga mata. Ina zuwa wani lokaci ma za su rika darewa madafun iko a matsayin zababbu

 

Iyalina

Ina tare da maigidana Alhaji Aliyu Abbani a yanzu haka ina da ’ya’ya hudu wadanda suke a raye. Akwai Muhammad Al’amin da Abubakar Sadik da Aliyu

Haidar da kuma A’isha (Hajiya Yaya)

 

Nasarorin da na samu

Alhamdulillahi, mun samu nasara. Abin da zan iya cewa na samu farin ciki wajen tallafa wa rayuwar wadansu mutane. Ba zan iya kirga mutanen da na zama sanadiyar sama musu aiki ko wadanda aka koya wa sana’o’i da ba su jari da sauransu ba. Ni ina kallon wannan a babbar nasara domin duk abin da mutum yake da shi idan bai taimaki mutane ba, to, abin ya zama ba ya da wata albarka.

 

Kalubale

Babu wani kalubale da zan ce na fuskanta sai na ’yan sa ido. Da kuma butulci daga mutane musamman irin wadanda aka kyautata wa a rayuwa. Ba abin bakin ciki kana tare da mutum  ka dauke shi da muhimmanci amma shi a bangarensa yana can yana yi maka zagon kasa. wannan yana daga cikin irin kalubalen da na fuskanta a rayuwa sai dai da yake akwai addu’ar iyaye da kuma tsarkakkiyar zuciya sai ki ga idan an dauko lamarin abin ba ya yin wani tasiri.

Burina

Babban burina shi ne in cika da imani Allah kuma Ya sa na ga Annabi Muhammadu (SAW). Sannan ina burin in ga Najeriya ta ci gaba ta kuma zauna a hade ba tare da raba ta ba. Ina kuma burin in ga Arewa da Jihar Kano sun ci gaba.

 

Abin da nake son bari a bayana

Ina son ko bayan raina a tuna da ni a matsayin wacce ta kawo alheri.

Mutane abin koyi

Ba ni da abin koyi sama da mahaifiyata Hajiya A’isha (Allah Ya yi mata rahama). Saboda mace ce jajirtacciya domin zan iya cewa duk da cewa mahaifinmu ya rasu tun ina da shekara goma, amma mahaifiyata ta jajirce har sai da muka yi karatu. Haka kuma ta yi mana tarbiyya kwarai da gaske domin ba ta bari mun sangarce don ba mu da mahaifi ba. Ko kallona ta yi da ido to zan bar abin da nake yi ballantana ta bude baki ta yi magana.

 

Shawarata ga mata

Ina shawararta ’yan uwana mata su zama masu hakuri da bin dokokin aure. Duk abin da mace za ta yi idan har ta rike wannan to za ta samu nasara. Idan mutum aka yi masa abu ya mayar da lamarinsa ga Allah. Haka kuma ina kiran mata da su nemi na kansu, yau idan ba ki samu, ba na tabbata gobe za ki samu.

Ina kuma shawartar mata ’yan siyasa cewa idan mutum yana son yin takara to ba rana daya kawai mace za ta zo ta ce tana son yin takara ba, dole sai ta fara shiga jam’iyya ta yi mata wahala tun daga kasa. Ma’ana ta shiga jam’iyya ta yi gwagwarmaya ta kuma bude hannunta. Na tabbata kafin ta yi batun takarar ma mutane ne za su nemi ta fito takara.  A hankali za ki ga mata sun samu suna ci gaba.