✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yancin mata a Turai da Musulunci (2)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga karashen rubutun da muka fara kawo muku a makon jiya. Ya ’yan uwa! Ku tuna…

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga karashen rubutun da muka fara kawo muku a makon jiya.

Ya ’yan uwa! Ku tuna cewa tun a karni na 5 Musulunci ya daukaka mace, daukakawar da ta kai in har mace ba ta da ra’ayin miji, to Musulunci ya ba ta damar ‘khul’i’ wato ta mayar masa da sadakinsa ko ta fanshi kanta su rabu. Ku sani a lokacin Jahiliyya, Larabawa sun kasance masu binne ’ya’yansu mata da ransu, sannan duk mutumin da aka haifa masa ’ya mace yakan yi fushi. Amma da Musulunci ya bayyana sai ya dakatar da duk wani nau’in wulakantawa, ya umarci  mata su rika sa sutura domin su wa kansu sutura ne, aka umarci maza su yi tsari ga matansu domin hana su gogayya da sauran maza wadanda ba maharramansu ba, aka umarci mazaje su nema wa mata ’yancinsu da abinci da sutura da kuma karantar da su ilimin addini, idan kuma mijin ba ya da damar karantarwa to ya kai su inda za a iya karantar da su.

Ya ’yan uwana mata! Ku tuna cewa a Madina wani sahabi ya saki matarsa sai kuma daga baya Allah Ya jarrabe shi da son ta fiye da kima, sai ya rika bin ta yana cewa ta yi hakuri ta dawo gare shi amma ta ki. Da Manzon  Allah (SAW) ya ji labari sai ya tausaya masa ya iske matar ya ce mata ya kamata ki yi hakuri ki koma gare shi. Sai ta ce ya Rasullilahi shin umarni ne ko kuwa shawara ce? Sai ya ce ina dai tausaya masa ne. Sai ta ce “A gaskiya ya Rasullilahi ba zan iya komawa gare shi ba.” Ku duba irin wannan fa?

Shin wane irin ’yanci ne Musulunci bai ba ku ba da har za ku kafa kungiyoyin kare ’yancin mata? Ku sani a Turai sai a tsakiyar karni na 20 suka samu ’yancin yin walwala da kubuta daga bauta daga hannun maza, ku kuwa Musulunci ya ba ku ’yanci tun sama da shekara dubu da 400 suka wuce, don haka ’yan uwana mata kada ku yarda da duk wata farfaganda a kan neman ’yanci, domin a zahiri Turai suna amfani da kalmar neman ’yanci ga al’ummar mata Musulmi ne domin ruguza kyakkyawar tarbiyyar Musulmi. Kuma makamin da suke amfani da shi na farfaganda ya fi makamin nukiliya barna, domin zai ragargaza koyarwar addinin  Musulunci,  wanda zai sa kafin mu farga mu gyara tuni mun makara.

A karshe ina fata ’yan uwana mata za su yi hattara.

Ado Musa Kaura Goje, Kano

Za a iya samunsa a lambar tarho: 08069186916