✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kara dakatar da Oshiomhole daga shugabancin APC

Kotu ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa. A ranar 4 ga watan Maris ne…

Kotu ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

A ranar 4 ga watan Maris ne Babbar Kotun Abuja ta dakatar da Oshiomhole daga rike matsayin bisa bukatar wasu ‘ya’yan jam’iyyar su shida daga Edo, jiharsa ta asali.

Daga baya Oshiomhole ya daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja yana kalubalantar hukuncin.

Sai dai a zamanta na Talata 16 ga watan Yuni, Kotun Daukaka Karar ta amince da hukuncin Babbar Kotun na dakatar da shi.

Alkalan Kotun su uku karkashin jagorancin Mai Sharia Monica Dongban-Mensem sun yi watsi da bukatar Oshiomhole ta soke dakatarwar bisa hujjar rashin kwakkwaran dalilai daga bangaren mai daukaka karar.

Hukuncin Kotun na zuwa ne a  ranar da Gwamnan Edo mai ci, Godwin Obaseki ya fice daga jam’iyyar APC bayan ta hana shi neman takarar zaben gwamnan jihar bisa zargin takardunsa na da matsala.

Obaseki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC ne bayan ganawarsa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari a Fadar Shugaban Kasa, domin neman mafita daga hana shi takarar.

Kwamitin Tantance ‘Yan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a jihar Edo ya ce ya hana gwamnan sake tsayawa takara ne saboda bambance-bambance da ya gano a takardunsa.

To sai dai ko kafin nan an dade ana zaman doya da manja tsakaninsa da Oshiomole, wanda ya nemi hana shi sake tsayawa takara.

Ko kafin zaben fid da ‘yan takarar, Obaseki ya yi zargin rashin samun adalci matukar tsohon ubangidan nasa na da ta cewa a harkar.

An dade ana takun saka tsakanin Oshiomhole da tsohon yaron nasa, lamarin da ya kai ga rabewar jam’iyyar APC a jihar Edo gida biyu.

Rikicin wanda ke da rasssa na daga cikin abubuwan da suka yi sanadiyyar shigar da karar kalubalantar rike shugabancin jam’iyyar da Oshiomhole ke yi.