✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yar Buhari ta koma cikin danginta bayan kwanaki 14 a killace

‘Yar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ta killace kanta bayan ta dawo daga kasar Burtaniya ta koma cikin ‘yan uwanta bayan gwajin da aka yi…

‘Yar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ta killace kanta bayan ta dawo daga kasar Burtaniya ta koma cikin ‘yan uwanta bayan gwajin da aka yi mata na cutar Coronavirus ya tabbatar da bata dauke da cutar.

A wata sanarwa da mai taimakawa uwargidan shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari, a fanin yada labarai Aliyu Abudullahi ya fitar a ranar Alhamis 2 ga wata Afrilu, ya shaida cewa ‘yar shugaba Buhari ta koma cikin danginta cike da koshin lafiya.

Ya ce yana farin cikin sanar da ‘yan Najeriya cewa, ta kammala kwanaki 14 a killace cikin koshin lafiya, inda mahaifiyarta Hajiya A’isha Buhari ta yi mata karba mai kyau.

A ranar 19 ga watan Maris ne uwar gidan shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari ta bada sanarwar cewa ‘yarta ta dawo daga Burtaniya kana ta killace kanta kamar yadda cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta NCDC ta zayyana.