Da Dumi Dumi

’Yar kwalisa za ta maka Cristiano Ronaldo a kotu

Yar kwalisa Andressa Urach, ’yar asalin Brazil a ranar Talatar da ta wuce ne ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf don maka shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid Cristiano Ronaldo a kotu saboda karyata batunta na cewa ya taba yin lalata da ita.
Ita dai ’yar kwalisar da ta yi suna a kasar Brazil inda wasu ke yi mata kirari da sunan Bum Bum ta ce ta kadu matuka a lokacin da ta ji dan kwallo Ronaldo ya fito kafafen yada labarai yana karyata batun ya taba yin lalata da ita inda ta yi alwashin gabatar da hujjojinta a gaban kuliya.  Shi kuwa Ronaldo ya ce ya lura ’yar kwalisar tana son yin amfani da sunan da ya yi ne dn ta samu daukaka a idon duniya kuma atafau shi bai taba yin latata da ita a kowane lokaci ba.
A ranar 28 ga watan Afrilun da ya gabata ne wata jaridar ta ruwaito labarin cewa Cristiano Ronaldo ya yi lalata da ita.
Sai dai jim kadan bayan da labarin ya bazu ne shahararren dan kwallon ya shiga kafar sadarwarsa ta Twitter da kuma Facebook ya karyata batun.
A watan jiya ne dan kwallon ya maka ta a kotu bisan zargin ta yi masa kazafi, ita kuma a yunkurin kare kanta ta ce yanzu haka tana shirin mayar da martanin maka  shi a kotu don ta tabbatar da ikirarinta na cewa babu tantama ya yi lalata da ita.
Cristiano Ronaldo dai ya yi kaurin suna wajen neme-neman mata a sassan duniya, kuma matashin dan kwallo ne da har yanzu bai yi aure ba.