Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
‘Yar Najeriya da aka sayar a matsayin baiwa ta dawo gida

‘Yar Najeriya da aka sayar a matsayin baiwa ta dawo gida

Wata ‘yar Najeriya da aka sayar a matsayin baiwa a kasar Lebanon, Temitope Ariwolo ta dawo gida a ranar Asabar.

An dawo da Temitope ne tare da wasu ‘yan mata ‘yan Najeriya ta filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Temitope da sauran matan sun samu tarba daga shugabar hukumar yaki da safarar mutane da kungiyoyin fararen hula da jami’an gwamnatin jihar Oyo da ‘yan majalisar wakilai.

An dawo da su ne sakamakon sa baki da gwamnatocin Najeriya da Lebanon suka yi tare da sauran masu ruwa da tsaki.