✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara biyar ta samu amsar wasikarta daga Sarauniya

Wata yarinya ’yar shekara biyar, Lyndsay Simpson ta rubuta wa Sarauniyar Ingila Elizabeth wasika kan burinta na mallakar agwagi ta rika kiwata su. Ala’amarin kuwa…

Wata yarinya ’yar shekara biyar, Lyndsay Simpson ta rubuta wa Sarauniyar Ingila Elizabeth wasika kan burinta na mallakar agwagi ta rika kiwata su. Ala’amarin kuwa ya faru ne bayan da mahaifiyar Lyndsay Simpson ta tabbatar mata da cewa Mai martaba Sarauniya ta mallaki daukacin agwagi, don haka sai ta samu izinin Sarauniya kafin ta ari guda. Ita kuwa yarinya sai ta aike da bukatar neman taimako ga sarauniya don ganin wannan buri nata da ya zame mata mafarki ya tabbata.

Lokacin da ta rubuta wasikar ba ta sa ran za a mayar  mata da amsa ba. Sai kwatsam ga wasika ta samu daga Sarauniya, al’amarin da ya cusa wa Lyndsay zumudi, har ma da mahaifiyarta, kuma an warware musu kullin da suka kasa warwarewa, wato zaton da suke yi na cewa sarauniya ta mallaki daukacin agwagi.

Jaridar The Times ta ruwaito cewa, ‘Jenie bine, maitaimakin jami’in aikewa da sakonni a Fadar Sarauniya ya ce Sarauniya ta tsaya tsaf wajen aikewa da sako ga Lyndsay kan bukatarta, sai dai labarin ba mai dadin ji ba ne gare ta.

“Sarauniya ta umarce ni in mika godiya gare ki kan wasikar da kika rubuto mata.. Daga Sarauniya wadda ta aiko miki da sako a natse kan kiwon agwagi.”

 “Ta yiwu in bayyana miki cewa abin da ake zato ba haka yake ba, cewa Sarauniya ta mallaki daukacin agwagin da suke Birtaniya. Mai martaba ta mallaki agwagi kadan kuma tana da iko ne kan agwagin da ke wani bangare na kogin thames. Za a iya tunawa cewa a matsayinsu na tsuntsayen daji, irin wadanan agwagin ana ba su kariyar hurumin doka da ta tanadar musu a karkashin dokar kula da halittun dawa ta shekarar 1981 (Wildlife and Countryside Act 1981).