Da Dumi Dumi

Yaran da suka sace dan shekara 5 sun toshe bakinsa ne ya mutu

Matasan da ake zargi da sace dan shekara biyar tare da hallaka shi a Kano
Matasan da ake zargi da sace dan shekara biyar tare da hallaka shi a Kano

Mahaifin yaron nan dan shekara biyar da wadansu samari uku suka sace shi suka nemi kudin fansa, Alhaji Ado Sulaiman Darmanawa ya ce samarin su toshe bakin dansa Ahmad Ado ne da salatef wanda hakan ya jawo ya rasu.

Marigayi Ahmad Ado wanda ake kira da Sayyid, masu garkuwa da shi sun kashe shi a makon jiya a daidia lokacin da suke kokarin karbar kudin fansa daga iyayensa.

Alhaji Ado Sulaiman Darmanawa ya shaida wa Aminiya cewa hakika ya ji takaicin yadda ya samu gawar dansa a sankame ba tare da ba ta wata kulawa ba. “Dukkan mai rai mamaci ne kowa yana sane  da hakan. Kuma na yi imanin Sayyad wannan rana ita ce ranar mutuwarsa tunda ta zo ba za a kara amsa ko sakan daya ba, amma abin takainci da damuwa shi ne hanyar da yaron ya rasu, domin yadda muka samu gawar a sankare ga kuma wani salatef a bakinsa abin ba kyan gani. Wannan shi ne babban abin da ya fi tayar min da hankali,” inji shi.

Mahaifin ya ce kasancewar akwai alaka ta jini da daya daga cikin yaran da suka yi garkuwa da marigayin da mahaifiyar marigayin hakan ya ba su damar gudanar da mugun aikinsu cikin sauki.  “Dana yana hannun surukata (kakarsa) ce, to a can yake makaranta saboda haka akwai almajirin da ke kai shi makaranta ya dauko shi idan an tashi. Wannan ne ya ba su damar sanin duk wani motsin da yaron yake yi,” inji shi.

Ya ce kwana uku kafin wannan waki’a ta auku masu garkuwa da yaron suka so sace shi sai dai ba su samu nasara a wancan lokaci ba. “Ba tare da sanin kowa ba kawana uku kafin su sace yaron shi dan uwan mahaifiyar yaron wato Ibrahim sai da ya shafe kwana uku yana kwana a cikin keke mai kafa uku da ake ajiye wa a kofar gidan. Da ya ga bai samu nasara a ba ana gobe lamarin zai auku sai ya zo gidan kakar yaron har sun yi barci domin ita sai farkwa ta yi ta gan shi a tsaye a kanta. Kin san da yake dan uwansu ne surukata duk da cewa ba ta ji dadin ganinsa cikin dare a gidan ba amma ta danne ba ta nuna masa ba. Sai da abin ya faru sannan ta gane manufarsa ta zuwa gidan cikin dare. Haka kuma da muka yi bincike mun gano Ibrahim din ne ya je har makarantar su yaron ya dauko shi da niyyar zai mayar da shi gida, shi kuma saboda ya san shi ya biyo shi daga nan ya yi tafiyarsa da shi ganin da ba a sake yi masa ba ke nan sai gawarsa,” inji mahaifin.

ADVERTISEMENT

Mahaifin yaron ya bayyana cewa bai san abin da ya faru ba sai waya suka yi masa cewa suna neman kudin fanar dansa da yake hannunsa “Da farko sai suka fara yi min waya inda suka ba yaron muka gaisa, sannan suka kashe wayar daga bisani su sake kirana suka gaya min abin da ake ciki tare da neman kudin fansa na Naira miliyan 20.  Har ma suna tsora ta ni cewa wai da manyansu ne da suke Zariya ko Zamfara to da Naira miliyan 50 za su nema idan kuma ba a ba su ba su kashe yaron. A nan na nuna musu ba zan iya biyan wannan kudi ba sai suka mayar Naira miliyan 10. Har suna yi min barazana cewa idan ban biya ba za su je makarantun sauran ’ya’yana su kwashe su. A nan suke gaya min cewa sun san cewa gidana ya fi karfin Naira miliyan 20. Ni kuma na gaya musu cewa ina da ’ya’ya da yawa ba zan iya sayar da gidana ba. A karshe suka ce in bayar da Naira miliyan 6. A nan ma na ki amincewa, a karshe dai muka yarda a kan zan biya Naira dubu 100,” inji shi.

Ya ce: “Can wajen Sallar Magariba sai suka kira ni cewa in kai musu kudin wani layi da ke kusa da Makarantar Hassan Gwarzo. Da na je sai suka kara tura ni wani wurin suka yi min waya cewa sun ga zuwana. Daga nan sai suka ce in kai wani wurin a nan dai unguwar inda kuma a nan ne aka kama su.”

Mahaifin ya ce ya sanar da ’yan sanda halin da ake ciki tun farkon lamarin inda hakan ya bayar da damar da ’yan sanda suka yi nasarar kama su bayan ya ba su lambar wayar da masu garkuwa da mutanen suka kira shi da ita, inda ’yan sanda suka rika bibiyar lamurransu har suka gano wurin da suke zaune.

Alhaji Ado ya ce “Bayan sun umarce ni in kai kudin kan wata bola a wani layi da ke unguwarmu sai na yi gagagwar sanar da ’yan sanda, don haka suka yi saurin isa wurin inda suka boye a wurin yadda ba za a gansu ba. Sai na tafi wurin na ajiye kudin a cikin bakar leda na yi tafiyata. Can sai ga daya daga cikinsu ya zo zai dauki jakar ’yan sanda suka fito daga maboyarsu suka kama shi. A nan aka tasa shi gaba ya je ya nemo sauran yaran biyu da suka kulla aika-aikar tare. A daren babu yadda ba a yi ba su fito da yaro amma abu ya gagara don haka ’yan sanda suka tafi da su hedikwata. To a can ne da suka fara dandana wuya daya daga cikinsu ya ce yaron yana binne a wani kango, aka taso su gaba aka zo da su suka nuna inda suka binne yaron a wani kango da ke unguwar. Da aka tone ramin wanda ke rufe da bulo-bulo sai ga yaron kwance a sankame bakinsa kuma rufe da salatef. Nan muka dauke shi inda aka yi masa sutura.”

Ya ce abin bacin rai shi ne “Duk da cewa suna sane da cewa dan ya rasu amma haka suka dage sai sun karbi kudi daga hannuna har suna yi min korafin wai duk shagunan da nake da su amma na kasa hada Naira dubu 100 cikin hanzari. Kodayake daga baya sun ce wai ganin yaron ya rasu ne ma dalilin da suka yarda za su karbi Naira dubu 100,” inji shi.

‘Abin da ya sa muka sace yaron’

Matasan masu garkuwa da mutanen sun ce bukatar kudi suke da ita shi ya sa suka sace dan don samun kudin fansa daga iyayensa.

Ibrahim Darmanawa wanda ya jagoaranci garkuwar da yanzu ke tsare da sauran biyun da suka taimaka masa wajen garkuwa da yaron ya ce ba su yi nufin kashe yaron ba, sai dai ajali da ya zo ya iske shi, “Domin abin da muka aikata shi ne mu karbi kudi daga hannun mahaifinsa saboda na san yana da kudi. Amma da na dauko yaron sai na mika musu shi ba na son ya gan ni domin zai gane ni, don haka su sauran abokan aikina suke kula da yaron. Ashe da ya fara jin yunwa ya gaya musu sai suka share batun, zuwa can yaro ya fara neman mafitar samun abinci sai suka sayo lemo suka zuba masa kwaya a ciki ya sha. Tun daga wannan lokacin kuma sai barci ya sace shi inda suka tafi da shi suka kwantar da shi tare da like bakinsa da salatef,” inji shi.

Ibrahim ya ce wannan ne karo na farko da ya taba shiga cikin wannan lamari, domin abokansa biyun ne suka nuna masa yadda harkar take shi kuma ya yi musu alkawarin dauko yaron musammam ganin mahaifinsa yana da hali.

Ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata  inda ya yi kira ga matasa da su nemi na kansu domin hakan shi zai kawo karshen zaman banza wanda shi ke sanya su gurbataccen tunani.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Haruna Kiyawa ya ce a halin yanzu wadanda ake zargin suna Sashen Yaki da Masu Garkuwa da Mutane don gudanar da bincike, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.

 

Share