✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarima Mohammed ya cika wasa lokacin karatu yana yaro – Malaminsa

Wani ma’aikacin BBC Rachid Sekkai wanda ya koyar da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman  harshen Ingilishi lokacin yana yaro ya bayyana rayuwar da Yariman ya…

Wani ma’aikacin BBC Rachid Sekkai wanda ya koyar da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman  harshen Ingilishi lokacin yana yaro ya bayyana rayuwar da Yariman ya rika gudanarwa ta dan gidan sarautar Saudiyya duk da cewa a lokacin ba a san shi ba sosai.

“Lokacin ina koyarwa ce a makarantar Al-Anjal da ke birnin Jeddah a 1996, sai kawai aka kira ni. Gwamnan Riyadh Yarima Salman bin Abdul Aziz Al Saud ya koma birnin Jeddah da iyalansa na wani lokaci, kuma yana bukatar malamin da zai koya masu Ingilishi.

“Mutumin da zai zama Sarkin Saudiyya daga baya ya tuntubi makarantar da nake koyarwa, kuma babu bata lokaci sai aka tura ni zuwa fadar Yariman domin in fara koyar da ’ya’yansa da matarsa ta farko ta haifar masa: Yarima Turki da Yarima Nayef da Yarima Khalid da kuma Yarima Mohammed.

Rachid ya kara da cewa, “A lokacin gidana na wata unguwa mai tasowa. Kullum da misalin karfe 7 na safe a kan aika wani direba ya kai ni makarantarmu ta Al-Anjal, inda bayan an kammala karatu da misalin karfe daya na rana sai direban ya kai ni fada. Da zarar an wuce kofar fadar da dakaru ke gadinta, motar da ta dauko ni kan wuce ciki ta gaban wasu maka-makan gidajen kawa da ma’aikata sanye da fararen kayan aiki ke lura da su. Akwai kuma motocin kawa masu yawa da aka ajiye su a gaban gidajen. Wannan ne lokacin da na ga motar nan mai suna Cadillac mai launin ruwan goro a karon farko.

“Bayan isa cikin fadar, sai Sarkin Fada na lokacin -Mansoor El-Shahry wanda da alama Yarima Mohammed mai shekara 11 da haihuwa a wancan zamanin ke matukar so ya yi min iso. Na kuma lura cewa Yarima Mohammed ya fi mayar da hankalinsa ga wasa da masu gadin fada maimakon koyon darussan da nake koya masa. Babu mai tsawata masa tunda shi ne babban yaya ga ’yan uwansa. Nakan samu natsuwar sauran kannen Yarima Mohammed ne idan ba ya nan. Amma da zarar ya isa dakin karatun sai komai ya watse,” inji shi.

Kuma, “Ba na mantawa kan yadda yake amfani da rediyon oba-oba da ya karba a hannun daya daga cikin masu gadin fada a lokacin da nake bayar da darussa. Yakan yi amfani da shi yana wasa da wadansu masu gadin, kana yana yi min shegantaka a gaban kannensa,” inji Rachid kamar yadda BBC ta ruwaito shi yana zayyanawa.