Da Dumi Dumi

Yariman Saudiyya ya dirar wa manyan ’ya’yan gidan saurata da ’yan siyasar kasar

Hukumomin Saudiyya sun kama uku daga cikin manyan ’ya’yan gidan sarautar kasar ciki har da dan uwan Sarki Salman bin Abdulaziz wato Yarima Ahmad bin Abdulaziz da Yarima Mohammed bin Nayef, wanda shi ne mai jiran gado kafin Sarki Salman ya tube shi ya kuma nada dansa, sai kuma Yarima Nawaf bin Nayef.

Rahotanni sun ce tsare wadannan mutane na daga cikin shirin Yarima Mohammed bin Salman na karfafa karfin fada-a-ji ganin tasirin mutanen da aka tsare.

A shekarar 2017 ne aka kafa wani kwamitin yaki da cin hanci da rashawa, a karkashin shugabancin Yarima Mohammed bin Salman mai shekara 32 a lokacin.

’Yan lokuta da sanar da kafa wancan kwamiti a lokacin, tashar talabijin ta Al Arabiya da ke karkashin masarautar ta sanar da kama wadansu ’ya’yan gidan sarautar11 da ministoci hudu da wadansu tsofaffin mutane da suka taba rike mukamai.

Wata majiya daga kasar ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) cewa hukumomin Saudiyya sun haramta wa wasu jiragen sama na wadansu attajiran kasar zirga-zirga, inda ake ganin hakan wata hanya ce ta hana su tserewa daga kasar.

ADVERTISEMENT

An yi imanin cewa Yarima Muhammed ya sanya a kame ’ya’yan sarautar ne da ake zarginsu da yunkurin yi masa juyin mulki daga cikinsu kuma akwai ’yan Amurka wadanda suka hada baki da jami’an kasashen waje.

An dai tabbatar da cewa Yariman Saudiyyar ne ya rattaba hannu a kan umurnin kama ’ya’yan sarautar kasar.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya