✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarinya ta daina tsoron ’yan sanda bayan shekara17 tana fama da matsalar

Matsalar tsoron ’yan sanda ta addabi wata matashiya mai shekara 21, tun tana ’yar shekara hudu a duniya, har ta kai ga mahaifin ya koka…

Matsalar tsoron ’yan sanda ta addabi wata matashiya mai shekara 21, tun tana ’yar shekara hudu a duniya, har ta kai ga mahaifin ya koka wa gidan rediyon Ajman radio 4 da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, don haka shugaban ’yan sandan Ajman da ya ji shirin ya umarci jami’ansa da su bi kadin lamarin, inda daga bisani aka tuntubi yarinyar da iyayenta, aka gayyato su zuwa ofishin ’yan sanda da ke Homaidiya. Kuma abin da suka yi mata ya kawo karshen wannan matsalar da ta addabeta tsawon rayuwarta

Daraktan ofishin ’yan sanda na AlHumaidiya, Laftanar-Kanar yahaya Al Matatroushi ya ce shugaban ’yan sanda yankin Janar Sheikh sultan Bin Abdullah Al Nuaimi ya bayar da umarnin ganin an warware matsalar da ta addabeta tun tana karama.

Likitan tabin kwakwalwa da ke kula da lafiyar yarinyar ya bayyana wa iyayenta cewa ba za ta samu sauki ba har sai ta fara ziyartar ofishin ’yan sanda sun saba, al’amarin day a yi musu nuni da cewa zai kawo mata sauyi a rayuwa. Don haka Al Matroushi da Kyaftin Ahmed Al Shamsi shugaban ’yan sandan asiri suka kewaya da yarinyar ofishinsu, inda akla gabatar da ita ga sassa daban-daban kan ayyukan da ’yan sanda ke gudanarwa. Sannan aka mika mata kyaututtuka, wadanda ta samu daga jami’an.

Bayan kammala ziyarar yarinyar ta nuna matukar farin cikinta danbgane da ta gani, inda ta yi ’yan sanda sayayyar kud-da-kud. Sannan ta yi godiya ga kwamandan ’yan sandan Ajman da ma’aikatansa da ke aiki a ofishinsa na Al Humaidiya, ta kuma yi masa fatan alheri kan ayyukan da suke gudanarwa.

Laftanar-Kanar Yahya Matroushi ya yi kira ga al’umma das u daina tsoratar da yara ’yan sanda, saboda lamarin na iya yin tasiri a rayuwarsu har ta kai ga sun yi wa jami’an ’yan sanda mummunar fahimta. “Ya kamata a fadakar da su kyakkyawar gudunmuwar da ’yan sanda ke bai wa al’umma wajen bayar da kariyar tsaro ga mutane,” inji shi.