Da Dumi Dumi

Yaro ya zama gwarzo bayan lashe gasar daga karfe

Lokacin da Timofey Klevakin mai shekara 11 ke daukar qarfe mai nauyin kilogiram 100
Lokacin da Timofey Klevakin mai shekara 11 ke daukar qarfe mai nauyin kilogiram 100

Yayin da mafi yawan yara ’yan shekara 11 suke karkata kan karatunsu na makaranta da gasar wasannin bidiyo wasu kuma gasar wasanni ta shafukan intanet, shi kuwa wani yaro mai shekara 11 a wani yankin karkara a kasar Rasha mai suna Timofey Klebakin, ya maida hankalinsa ne kawai a harkar motsa jiki da daga karafa masu nauyi, hakan ya sa ya kafa tarihi.

Timofey, dai tun yana dan shekara biyar yake da sha’awar daga karafa masu nauyi saboda ya kasance yana kallon mahaifinsa a duk lokacin da yake motsa jiki a cikin gida da ke kauyen Shalya a tsibirin Ural. Bayan mahaifin Timofey Klebakin, mai suna Arseny Klebakin ya fara horar da dan nasa duk da rashin amincewar mahaifiyar dan nasu ganin cewa ya nada karancin shekarun da zai fara horar da shi irin wannan motsa jikin.

A lokacin da Timofey, yake shekara shida an gudanar da gasar daukan abu mai nauyi, sai Timofey ya bai wa wadanda suka halarci gasar mamaki, inda alkalan gasar suka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe gasar daukan abu mai nauyin kiligiram 55, tun wannan lokacin Timofey, ya ci gaba da kwazo a yanzu da ya kai shekara 11 ya shiga kundin tarihi  bayan ya lashe gasar daukan nauyin kilogiram 105.

A shekarar 2019 aka yi gasar kofin Asiya wanda aka yi birnin Chelyabinsk, inda Timofey Klebakin ya samu nasarar lashe gasar daga karfe mai nauyin kilogiram 100, hakan ya birge mahalarta gasar saboda karancin shekarunsa da kuma yanayin jikinsa kamar ba zai iya lashe gasar daukan karfen da nauyinsa ya kai wanda ake gasar ba. A irin shekarun Timofey, bai wuce ya dauki karfen da ya kai Kilogiram 35.

Amma abin ban sha’awar shi ne, bayan motsa jikin da yake yi, yana atisayen daga tayar motar tarakto wasu lokutan da kuma kokarin jan kananan mota ta hanyar amfani da igiya. A kauyen su Timofey, ya kasance gwarzo saboda yana iya yin abin da wasu matasan da suka wuce shekarunsa basa iya yi kuma yana iya shiga gasar da matasan da suka girme shi.

ADVERTISEMENT

Abin da ya fi daukar hankalin jama’a shi ne a lokacin da sa’o’in Timofey, suke wuraren wasanni shi kuwa burinsa ya zama gwarzo a gasar da yake shiga, a kalla yana atisaye sau uku a duk mako.

Mahaifiyar Timofey, tare da wasu masana harkokin yara sun nuna damuwarsu game da yanayin kalubalen lafiyar jikin yaron nan gaba. Sai dai mahaifin Timofey, ya ce yana kokarin horar da dansa ta yadda atisayen ba zai cutar da shi ba, duk da sha’awar da yake da shi a zuciyar shi.

A yanzu haka Timofey Klebakin, yana samun horo na musamman don shiga gasar da gasar ‘Russian Championship’, da za a yi nan gaba na daukar karfe mai nauyin kilogiram 105.

Share