Aminiya

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda zai fara daga ranakun 23 ga Oktoba 2019 zuwa 26.

Za a gudanar da taron ne tsakanin Rasha da kasashen Afirka. Inda za a tattauna kan batutuwan da suka jibanci harkar tsaro, kasuwanci, kimiyya da fasaha, samar da iskar gas da dai sauransu.

ADVERTISEMENT

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu, ne ya sanar da hakan.

A yayin taron Shugaba Buhari zai gana da takwaransa na Kasar Rasha Vladimir Putin.

ADVERTISEMENT