✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yau za a daura auren Adamu Nagudu: Gobe kuma Ahmad M. Sadik zai angwance

A yau Juma’a za daura auren fitaccen mawaki Adamu Hassan Nagudu da Zainab Zakari Ya’u da misalin karfe 2:00 na rana a garin Jos da…

A yau Juma’a za daura auren fitaccen mawaki Adamu Hassan Nagudu da Zainab Zakari Ya’u da misalin karfe 2:00 na rana a garin Jos da ke Jihar Filato.
A gobe Asabar kuma Sharararen mawaki Ahmad M. Sadik da ya yi wakar ‘Bashin Gaba’ zai angwance.
Za a daura aure mawakin ne da Nana Barira Sa’ad Yakubu a Gidan Malam Sa’ad Mai Zabi da ke Hayin Ojo Tankin Toliya Sabon Gari, Zariya, da misalin karfe biyu na rana. Daga nan za a yi liyafa a ranar Lahadi 16 ga watan Yuni, 2013 a Darul Tauhid daura da Jifatu Departimental Store da ke Zariya Road a Kano.