Search
Subscribe
Yau za a fara gasar cin kofin duniya na mata

Yau za a fara gasar cin kofin duniya na mata

A yau Juma’a ake sa ran za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na mata a Faransa.

Kasashen da za su fafata a yau sun hada da mai masaukin baki Faransa da kuma Korea Republic.  Za a yi wasan ne da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya.

Sai dai a gobe ne ’yan matan Najeriya za su kece-raini da  ’yan matan Norway da misalin karfe takwas na dare agogon Najeriya.

Najeriya dai za ta fafata ne a rukunin A da kasashen Faransa da Norway da Korea Republic.

Sannan kasashe uku ne suke wakiltar Nahiyar Afirka da suka hada da Najeriya da Afirka ta Kudu da kuma Kamaru.

Sannan manyan kasashe irin su Brazil da Italiya da Sifen da Japan da sauransu duk suna cikin wannan gasa.

Babu wata kasa daga Afirka da ta taba daukar wannan kofi.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin