✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a fara Gasar La-Liga ta Sifen

A yau Juma’a ne ake sa ran za a fara gasar La-Liga ta Sifen. Idan za a tuna a makon jiya ne aka fara gasar…

A yau Juma’a ne ake sa ran za a fara gasar La-Liga ta Sifen. Idan za a tuna a makon jiya ne aka fara gasar Firimiya ta Ingila inda a wannan mako za a yi wasa na biyu.

Kamar yadda jadawalin gasar ta La-Liga ya nuna, yau Atletico Bilbao za ta kece-raini da FC Barcelona da misalin karfe 8 na dare agogon Najeriya.

A gobe Asabar kuma kulob din Celta Bigo zai shawo ta da na Real Madrid da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya.  Sannan jibi Lahadi kuma kulob din Atletico Madrid zai hadu da Getafe.

Wadannan wasanni na daga cikin wadanda za su fi zafi a wannan mako.

Idan za a tuna kulob din FC Barcelona ne ya lashe gasar a bara.

Sai dai a bana akwai alamun kulob da dama sun shirya wa gasar don ganin sun taka wa Barcelona birki kamar yadda Barcelona ta shirya ci gaba da kare kambinta.