Aminiya

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi.

Babban alkalin jihar Nasir Ajanah, ya halarci zauren taro na Banquet Hall da ke gidan gwamnatin jihar da ke Lokoja babban birnin jihar don rantsar da Edward.

ADVERTISEMENT

A yau Litinin ‘yan majalisar dokokin jihar suka tantance Edward, bayan ya gabatar da kansa a gaban zauren majalisar.

Za a rantsar da Edward a matsayin sabon mataimakin Gwamnan jihar ne bayan tsige tsohon mataimakin gwamnan jihar Simon Achuba, da majalisar dokokin jihar ta yi.

ADVERTISEMENT