✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaushe jam’iyyun siyasa za su daina kama-karya?

A tawa guntuwar fahimtar kan al’amuran siyasar da ke wakana a kasar nan, sai nake ganin ko daga farkon wannan Jamhuriya ta Hudu da sojoji…

A tawa guntuwar fahimtar kan al’amuran siyasar da ke wakana a kasar nan, sai nake ganin ko daga farkon wannan Jamhuriya ta Hudu da sojoji suka mai da mulkin dimokuradiyya a 1999 zuwa yanzu, ya ci a ce masu tafiyar da mulkin sun koyi darasin da za su rika bari jama’a suna yanke hukunci ak an wanda ya cancanci ya tsaya zabe, da wanda za a nada da wanda za a hana tsayawa takara kwata-kwata.

Abin da ya sanya na ce haka bai rasa nasaba da irin yadda babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta share shekarA 16 tana mulkin kasar nan, , amma ta fadi a babban zaben 2015, wanda ita da kanta bayan ta rasa mulki ta amince cewa karfa-karfa da kama-karyar da ta rika yi a cikin mulkinta  ne ya haddasa ma ta waccan faduwa.

A ’yan watannin nan ne bayan ta farfado daga rikicin cikin gidan da ya yi mata katutu a bayan faduwa zaben da kuma niyyarta ta tunkarar zabubbukan 2019 da take kwadayin dawowa kan karagar mulki, aka ji shugabanta na kasa, Mista Uche Socondus, yana baiw a ’ya’yan jam’iyyar da sauran jama’ar kasa hakuri da neman afuwarsu a kan danyar da ta tafka lokacin mulkinta, tare da ba da tabbacin ba za su sake tafka irin wadancan kura-kuran ba muddin jama’ar kasa suka sake zabensu.

Duk da ba da wancan tabbaci da neman afuwa, yanzu da ake cikin jajibirin zabubbukan 2019, ’ya’yan jam’iyyar da sauran ’yan kasa suna ta ganin sabarta-juyarta da take ta faruwa a cikin jam’iyyar ta PDP. Alal misali dauki abin da ke faruwa a jihohin Kano da Ebonyi da Gombe da Nasarawa da Kuros Ribas da sauransu.

A Jihar Kano, canjin shekar da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da wadansu daga cikin ’yan majalisar dokoki ta kasa da na jihar mabiya darikar siyasarsa ta Kwankwasiyya daga APC zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ta sanya, uwar jam’iyyar ta kasa, ta mika masa ikon jan ragamar jam’iyyar reshen jihar da yanzu ya ba shi damar sai wanda ya ga dama zai ba takarar neman mukamin Gwamnan Jihar da wanda zai rufa masa baya da ’yan majalisar dokoki na kasa da na jihar.

Hakan ta sa tsohon Gwamnan Jihar kuma tsohon Minista Malam Ibrahim Shekarau da a shekarar 2014, bayan sun kafa Jam’iyyar APC, Sanata Kwankwaso yana Gwamnan Jihar, APC din ta ba Gwamna Kwankwaso jan ragamar jagorancin jam’iyyarta APC a jihar, wanda ala tilas Malam Shekarau ya koma PDP. To yanzu ma PDP ta kwata abin da APC din ta yi a Kano.

A Jihar Nasarawa ma Sanata Solomon Ewuga ake rade-radin PDP, za ta ba takarar neman mukamin Gwamnan Jihar, alhali jam’iyyar tana da mutum 7 da tuni suka nuna kwadayinsu kan su tsaya wannan takara, wadanda yanzu ake cewa dukansu sun yi fatali da wancan yunkuri na uwar jam’iyyarsu ta kasa. Haka ake da irin wadannan labaran a jihohin Kuros Ribas da Sakkwato da Gombe.

Ita kuwa babbar jam’iyya mai mulki ta APC, babbar annobar da ta auka mata, ba ta wuce ta irin yadda wadanda suke cikinta da masu hankoron komawa cikinta kowa ke neman ya ga ya samu tikitinta ne kawai da wuya, amma ba wai cin zabe ba. Hakan ta sanya baki biyun da shugabancin jam’iyyar na kasa ya yi tun bayan taron Kwamitin Zartarwa na kasa a kwanakin baya cewa lallai kowane reshen jiha na jam’iyyar ya gudanar da zabubbukan fitar da ’yan takararsa ta hanyar ’yar tinke daga bisani kuma ya dawo ya ce  kowane reshe kuma yana da zabin ko ya yi tsarin zaben ’yar tinke ko na wakilai koma ta hanyar samun fahimtar juna da za a karkare ta hanyar daga hannu.

Wannan ya sanya tun farko mafi yawan gwamnonin jam’iyyar suka ja daga suka ce ba za su yi zaben ’yar tinken ba, sun gwammace su yi amfani da na wakilai ko kuma ta amincewa. Zuwa yanzu jihohin Kano da Abiya kadai suka ba da shelar za su gudanar da zaben ’yar tinken. Jihohi irin su Kebbi da Ebonyi kuwa cewa suka yi za su gudanar da zaben ta hanyar maslaha, wato daga hannu. A jihohin  Sakkwato da Katsina da Imo da Kogi da Ondo da Adamawa da Zamfara da Yobe duk gwamnoninsu sun kafe a kan lallai tsarin zaben yin amfani da wakilai za su yi.

A jihohi irin su Zamfara da Yobe da Imo da Ogun makamantansu da zuwa yanzu gwamnoninsu sun ayyana wadanda za su gaje su, su kuma sun ayyana kansu  don takarar mukaman da suke son su zarce ce a kansu bayan sun kammala wa’adinsu na zango na biyu. Wannan kama-karya na wadansu gwamnonin APC, suka sanya  a wadancan jihohi da makamantansu ana can ana ta ka-ce-na-ce a tsakanin gwamnonin da jiga-jigan jam’iyyar da suke da sabanin ra’ayi da su, har ta kai wadansu sun kai kara ga uwar jam’iyyar APC ta kasa, suna neman ta sa baki, kuma ta tabbatar an yi zabubbukan a kan tsarin da kowane dan takara zai ji an yi da shi.

Idan har shugabannin manyan jam’iyyun nan biyu, sun yi imanin cewa mulkin dimokuradiyya mulki ne na jama’a, daga jama’a kuma don jama’a, to lokaci ya yi da za su fara karatun ta-natsu, su rika barin ana fitar da ’yan takarar da jama’a suka ce suna so, koda kare ne, idan jama’ar suna zaben karen. Lokacin da kuma suka ji ba sa sonsa kuma su canja da wanda suke so, ai batu a ke na ba kowa dama.

Na san shugabannin jam’iyyun siyasar kasar nan sun fi ni sanin cewa irin wannan kama-karya da nuna isa, suke kan gaba wajen rura irin rigingimun siyasar da aka dade ana fama da su. Rigingimun da suke haddasa gaba da kiyayya da kashe-kashen rayukan al’umma da dukiyoyi. Saura da me? Shawara ga masu kada kuri’a, wadanda da bazarsu ake rawa, ita ce kowa ya tanadi katinsa na kada kuri’a, ta yadda a ranakun zabe kuma ya aje son zuciyarsa da tunanin wanda zai ba shi kudi, ko wani abu na rayuwar duniya, ya zabi sahihi kuma mai gaskiya da rikon amana a zaman wakilinsa. Ta haka kadai nake ganin za mu kai ga gaci. Allah Ya taimake mu, wajen dawowa daga rakiyar masu hankoron sai sun mallake mu ko ta halin kaka a kasar nan.