✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yawaitar bindiga a hannun jama’a ba alheri ba ne – Kanar Abdu

Wani tsohon soja mai ritaya, Kanar Muhammadu Abdu da ke Kaduna, ya ce masu mallakar bindiga saboda kariyar kai ba su san mai ake kira…

Wani tsohon soja mai ritaya, Kanar Muhammadu Abdu da ke Kaduna, ya ce masu mallakar bindiga saboda kariyar kai ba su san mai ake kira bindiga ba. Ya ce idan mutum yana da bindiga akwai bukatar ya koyi yadda ake amfani da ita sannan ya tabbatar yana da iznin mallakarta. “Wanda bai san sirrinta ba ce yake irin wannan magana cewa wai ya mallake ta ce saboda kariyar kai,” inji shi.

Kanar Abdu ya ce akwai tsarin aiki ko amfani da bindiga domin aba ce da ke da tsari na amfani da ita. “Mutane sun jahilci abin ne kawai kuma ita bindiga kafin ka yi amfani da ita sai ka koyi yadda ake sarrafa ta. Su masu mallakar bindiga a yanzu a ina suka koyi amfani da ita. Ko a ina suka koyi harbi? Idan ba ka Koya ba babu yadda za ka yi amfani da ita yadda ya dace. Saboda haka dole sai an koyi kowace irin bindiga ce kuwa. Sannan gaskiya akwai bukatar sai dokar kasa ta amince da rike bindiga in ba haka ba duk wanda ya mallake ta ya saba wa dokar kasa,” inji shi.

Ya ce mallakar bindiga akwai babban hadari “Domin idan aka ce kowa ya mallaki bindiga ko fada ka yi da mutum sai ya harbe ka, kai wani ko musu kuka yi sai ya dauki bindiga ya harbe ka. Saboda haka dole ne abi doka a zauna lafiya. Sannan akwai bukatar gwamnati ta sake yin yekuwa cewa duk wanda aka samu da bindiga ba tare da izni ba doka za ta hukunta shi. Dole ne mutane su fahimci haka saboda a zauna lafiya domin a yanzu duk matsalolin rashin tsaron da muke fama da su a kasar nan suna da alaka da yawan bindiga da mutane ke mallaka ba bisa ka’ida ba,” inji Kanar Abdu.