✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan Kudin Haraji: ’Yan kasuwar Shaikh Gumi Kaduna sun yi zanga-zanga

Wasu daga cikin ‘Yan Kasuwar Shaikh Abubakar Gumi da ke jihar Kaduna sun yi zanga-zanga saboda yawan haraji da kudin shago da suka ce, Hukumar…

Wasu daga cikin ‘Yan Kasuwar Shaikh Abubakar Gumi da ke jihar Kaduna sun yi zanga-zanga saboda yawan haraji da kudin shago da suka ce, Hukumar Kula da Kasuwar na amsa a hannunsu.

‘Yan kasuwar rike da ganye sun rufe titin da ya bi ta shataletalen leventis suna cewa, basu so ba. Sun yi zanga-zangar ne da misalin karfe 12 na rana.

Aminiya, ta samu labarin cewa an tura jami’an tsaro wurin inda suka tsaya nesa da inda ‘yan Kasuwar ke zanga-zangar.

Daya daga cikin shugabannin kasuwar Alhaji Lawal Umar Adam, ya ce ‘yan kasuwa na daya daga cikin wadanda gwamnatin jihar ke wulakantawa duk kuwa da kasancewar suna daga cikin wadanda suka mara masu baya lokacin zaben da ya gabata.

Sai dai Barrista Muhammad Sani, wanda shi ne sakataren Hukumar Kasuwar ya karyata zargin cewa, suna tsauwalawa ‘yan kasuwa haraji ya ce, bayan kudin shago da suke karba sai kudaden kulawa da Kasuwar kuma duk a cewarsa babu wanda aka kara.

Dan haka ya ce, tuni sun gana da shugabannin ‘yan kasuwar kuma komai sun samu matsaya har an bude shaguna domin ci gaba da harkar kasuwanci.