Da Dumi Dumi

Yawan wadanda Coronavirus ta kama a Najeriya ya kai 30

Wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya sun kai 30

Yawan mutanen da aka tabbatar suna dauke da kwayar cutar Coronavirus a Najeriya ya cika 30 bayan da aka samu wasu sababbin kamuwa uku a Legas.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta ce biyu daga cikin mutanen daga kasashen waje suka dawo, yayin da na uku kuma ya yi hulda da wani mai dauke da cutar.

“Zuwa karfe 5.28 na yammacin ranar 22 ga watan Maris, mutum 30 ne aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya”, a cewar hukumar.

Tuni dai aka sallami biyu daga cikin mutanen 30 bayan sun warke, yayin da 28 ke samun kulawa a wuraren da aka kebe.

Da safiyar ranar Lahadi ne dai aka samu Karin mutum daya da aka tabbatar yana dauke da cutar a Abuja.

ADVERTISEMENT

Hukumar ta NCDC dai ta ce a yanzu haka tana da dakunan bincike guda biyar a fadin Najeriya wadanda ke da kayan aikin da za su iya gwaji don gano cutar.

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya