✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawan wadanda suka kamu da Coronavirus ya kai 131

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da Coronavirus a Najeriya ya karu zuwa 131 yayin da aka samu karin mutum guda wanda ya rasu sakamakon…

Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da Coronavirus a Najeriya ya karu zuwa 131 yayin da aka samu karin mutum guda wanda ya rasu sakamakon cutar.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta bayyana hakan a lokacin da take sanar da samun sabbin kamuwa mutum 20.

“An bayar da rahoton samun sabbin kamuwa da COVID-19 a Najeriya mutum 20, mutum 13 a Legas, hudu a Yankin Babban Birnin Tarayya, biyu a Kaduna, daya a Oyo.

“Zuwa karfe 9.00 na daren 30 ga watan Maris, an tabbatar da mutane 131 sun kamu, yayin da mutum biyu daga ciki suka riga mu gidan gaskiy”, inji sanarwar.

Daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu sun kamu a Jihar Kaduna har da Gwamna Nasiru El-Rufai.

Ga adadin da jihohi suke da shi na wadanda aka tabbatar sun kamu: