✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yawancin fim din kamfanina na al’ada ne – Alhaji Sani Sule Katsina

Alhaji Sani Sule Katsina shugaban Kamfanin Rite Times Multimedia, fitaccen dan kasuwa ne da ke harkokin shirya Fina-finan Hausa, sannan kuma shi ne Sakataren Kungiyar…

Alhaji Sani Sule Katsina shugaban Kamfanin Rite Times Multimedia, fitaccen dan kasuwa ne da ke harkokin shirya Fina-finan Hausa, sannan kuma shi ne Sakataren Kungiyar Masu Shirya Fina-Fina ta Arewa wato Arewa Film Makers Association AFMAN. A hirarsa da wakilinmu ya ce bayan harkar fim ya kafa gidauniya da yake amfani da ita wajen tallafa wa matasa domin inganta rayuwarsu, inda har kamfaninsa ya samu kyautuka da lambobin yabo da dama a gida da waje. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Gabatar da kanka ga makaranta wannan jarida.

Alhaji Sani Sule Katsina: Sunana Alhaji Sani Sule Katsina Sakataren kungiyar masu shirya Fina-Fina ta Arewa wato Arewa Film Makers Association of Nigeria AFMAN.

Aminiya: Yaya ka shigo harkar shirya Fina-Finan Hausa?

Alhaji Sani Sule Katsina: Na fara ne da matsayin mai shirya wa babban darakta fim, da yake na shigo harkar da kudi na ne, inda nake sanya wa fim domin neman riba, kuma daga wancan lokaci zuwa yanzu na ta samun riba har Allah Ya kawo ni wannan matsayin na mai shirya fim da kansa a kamfanina na Rite Times Multimedia.

Alhamdulillahi! Ni tsohon ma’aikaci ne a Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi a Legas, na ajiye aikina na fara kasuwanci har Allah Ya kawoni wannan matsayi da nake ciki har kar fim. Kuma ina godiya ga Allah

Aminiya: Ana samun korafi wasu masu shirya Fina-Finai ba sa sanya wakoki da raye-raye da ke nuna al’adun Hausa-Fulani sai ku rika kwaikwayon rawa da wakokin Indiya.?

Alhaji Sani Sule  Katsina: To Gaskiya mai yiwuwa wannan ba gaskiya bane saboda duk wanda ya san lamfanin Rite-Time Multimedia ya san mafi yawancin Fina-Finan mu duk na al’ada ne. Misali ka ga film din Kukan Kurciya na al’ada ne, kuma muna shirya Fina-Finai na musulunci muna kuma koya wa mata Sana’a kai Fina-Finai masu yawa da muka shirya muna ilimantar da mutane. Kamar wani film din mu da muka shirya na yara wanda kwanan nan za mu fara nuna shi.

Aminiya: Duk da irin wannan hobbasa ko akwai wata kungiyar da ta taba karrama kamfaninka?

Alhaji Sani Sule Katsina: Eh! Akwai wata kungiya a kasar Amurka mai suna Zumunta Association, sun taba karramani sannan akwai mujallar African Boice Magazine, sun bani kyautar Gwarzon wanda ya fi iya shirya Fina-Finai.

Aminiya: Wane kalubale kake fuskanta?

Alhaji Sani Sule Katsina: Koda yake gaskiya mutum ba zai ce ba ya fuskantar kalubale ba a rayuwa, sai dai Alhamdulillahi duk sana’ar da mutum yake yi kuma ya riketa tsakaninsa da Allah, to Allah zai taimakeshi.

Aminiya: A bangaren nasarori fa?

Alhaji Sani Sule Katsina: Na samar da wata gidauniya da take taimakawa wajen samar wa matasa ayyukan yi. Zuwa yanzu na samar wa sama da mutum 1,000 ayyukan yi tsakanin jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina da sauran duk inda muka je aikin film. Kaduna kusan ko ina muka je muna hada wa da matasa mu ba su aikin yi.