✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaya kuke ganin dakatarwar da aka yi wa Babban Jojin Najeriya?

A makon jiya ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Walter Onnoghen daga mukaminsa har sai an gama bin…

A makon jiya ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Walter Onnoghen daga mukaminsa har sai an gama bin kadin shari’arsa ta tuhumar kin bayyana kadarorinsa da ya yi. Matakin ya jawo muhawara a tsakanin al’ummar Najeriya da na waje. Aminiya ta ji ta bakin jama’a kan lamarin kamar haka:

 

Wannan mataki darasi ne ga shugabanni– Auwalu Sharubutu

Daga Hussaini Isah, Jos

Auwalu Sharubutu Mai Siminti: A ra’ayina, wannan dakatarwa da aka yi wa Babban Jojin Najeriya daidai ne. Domin dokar Najeriya ce ta bayar da umarnin idan aka ba ka mukami, ka bayyana yawan dukiyar da ka mallaka a cikin gida da wajen Najeriya. A lokacin da aka naca Babban Jojin nan, an bukaci ya bayyana kadarorinsa, amma sai ya ki facin gaskiya. Don haka wannan dakatarwa da aka yi masa ta yi daidai. Masu suka da maganganu kan wannan al’amari suna facar ra’ayinsu ne kawai, ko suna sanya siyasa ce kawai. Wannan mataki da Shugaban Kasa ya cauka doka ce kawai ta yi aikinta. Kuma wannan mataki zai iya zama darasi ga wacansu shugabanni da suka ki bayyana dukiyoyinsu a Najeriya bayan gwamnati ta ba su mukamai.

 

Dakatar da shi ci gaban dimokuraciyya ne– Ado Lawal

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Ado Lawal: Duk da cewa ana lokacin zabubbuka ne da ba za ka iya hana mutane facar ra’ayinsu ba cewa hakan ba ya rasa nasaba da siyasa, amma gaskiya a ra’ayina wannan dakatarwar ci gaba ne a harkar dimokuraciyya lura da irin karfin da bangaren shari’a ke da shi wanda in aka bari ya gurbace to kasar ta gama lalacewa ke nan. Duk da na ga da yawan lauyoyi na nuna damuwarsu da wannan dakatarwar amma a ganina wannan wata gata ce hatta a wurinsu don wata rana su ne za su rika kafa hujja da ita. A bari a gama bincike tukunna. Sai dai kirana ga gwamnati shi ne, idan har sun gama bincikensu tsakani da Allah kuma babu wata hujja ta shari’a da za a tsige shi a dawo da shi, in kuma shari’a ta ci shi shi ke nan, ka ga kowa sai ya shiga taitayinsa ke nan a cikin alkalan.

 

Ina goyon bayan matakin – Nasiru Ibrahim

Daga Abbas Calibi,  Legas

Nasiru Ibrahim Gulma: Ni nawa ra’ayin shi ne, ba zan so in yi riga malam masallaci ba, kodayake shi kansa Babban Jojin ya amince da wasu tuhumar da ake yi masa na rashin facin wasu kadarori ko kucacen da ya mallaka. Kuma a fahimtata wannan babban abin kunya da ya yi har wcansu daga cikin kabilarsa suna yin wasu maganganu na nuna cewa da sauran rina a kaba. Domin gwamnatin baya ta cire wacansu alkalan ba tare da bin tsarin doka ko tuhumarsu da wasu laifuffuka ba, sai dai domin biyan bukatarsu, kuma a wannan gwamnatin ai an cire Shugaban Hukumar DSS, me ’yan Arewa suka ce? Saboda haka ne ya sa muke mara wa Shugaban Kasa baya domin nuna ba sani ba sabo a kan duk wanda ya keta doka. Kuma dakatar da shi ta yi daidai domin nuna kafar angulu da yake son ya yi wa wannan gwamnati da ta aza shi a kan wannan mukami. Don haka muna goyon bayan dakatarwar da aka yi masa.

 

Ba a bi ka’ida ba – Barista Omodolapo

Daga Abbas Calibi, Legas

Barista Omodolapo Yusuff: Ni a ra’ayina, ba a bi tsarin doka wajen dakatar da Babban Jojin Najeriya ba, kodayake mu a kasar nan ba a caukar tarihi da muhinmmanci, zan so in tunatar da mu cewa a baya a 1998 tsangayar lauyoyi da ke karkashin Mai shari’a Kayode Esho sun bukaci ko sun ba da shawarar a kori ko a cire Onneghen daga mukaminsa na Alkalin Kotun Koli, amma abin mamaki ba a bi shawararsu ba. Wannan mutum shi ne har ya zo ya zama Babban Jojin Najeriya, ka ga tun ranar gini tun ranar zane ke nan. Amma abin takaicin shi ne, hanyar da aka bi wajen dakatar da shi ta saba wa ka’idar shari’a ko tsarin dokar kasa, ba a bi tsarin doka ba kuma idan har za a ce ya amsa tuhumar da ake masa to akwai maganar shi ma a saurare shi ya kare kansa kafin a cire shi. Bai kamata Gwamnatin Tarayya ta rika yi wa tsarin shari’a hawan kawara ba, ta yadda suke bin dokokin da ransu ya so sannan su sanya kafa su yi fatali da wacanda ba su kwanta a ransu ba. Misali, abin da ya faru da Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ba su yi komai ba, sun tafi batun Onnoghen. Ka ga wannan ya nuna cewa suna zaben abin da suka so ne su yi hukunci a kansa. Daga karshe idan har masu madafun iko suna yi wa tsarin dokar kasa cin kashi in ’yan siyasa suka yi wa talaka cin fuska ina zai je? Idan tsarin shari’ar kasa ya yi rauni, ina talaka zai je a share masa hawaye?

 

Ba na goyon bayan dakatarwar – Umar Farouk

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Umar Farouk: “Gaskiya a ra’ayina wannan dakatarwar ba a yi ta a lokacin da ya dace ba, wanda hakan shi ke taimakawa wajen cusa siyasar kabilanci da addini da raba kan ’yan kasa. Yanzu babu abin da za ka faca wa ’yan adawa su yarda kan dalilin dakatar da Onnoghen kuma komai gaskiyar wannan ba za su aminta da shi ba kamar yadda su kuma magoya bayan duk wani abu da Shugaba Buhari zai aiwatar ba sa goyon bayan Onnoghen komai rashin kyautawar da ba a yi masa ba. Domin har wasunsu ma na cewa wai gwamnati ta hango ’yan adawa za su yi amfani da shi ne suka fake da zartar da wannan matakin dakatarwar har sai bayan zabubbuka in ma a dawo da shi ko a sallame shi. Maganar gaskiya ita ce, me ya sa tuntuni ba a cauki wannan mataki ba sai yanzu? Kuma hukunci nawa ne kotu ke cauka gwamnati ke kawar da kai ba ta gaggawar zartar da shi?

 

Shugaban Kasa ya yi daidai – Manu Isah

Daga Hussaini Isah, Jos

Malam Manu Isah Idris: A ra’ayina, dakatar da Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Walter Onnoghen da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, daidai ne. Domin ya bi umarnin Kotun Ca’ar Ma’aikata ce da ta ce ya yi haka. Don haka Shugaban Kasa bai yi laifi ba. Saboda babu yadda za a yi a naca mutum a matsayin mai tuhumar masu laifi, sannan  a zo a same shi cikin masu laifin. Kuma maganganun da wacansu ke yi kan al’amarin, musamman Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka suna yi wa Najeriya katsalanda ce kawai. Domin idan aka duba, a kasashensu  zargi kawai za a yi wa mutum, sai ka ga ya sauka daga kan mukaminsa. Kuma maganganun da wacansu ’yan Najeriya suke kan al’amarin, suna yi ne don sun ga lokacin zabe ya zo, don haka suke son su yi amfani da wannan dama su saka siyasa a ciki.