✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaya Toure ne Gwarzon dan kwallon Afirka Na BCC a bana

Shahararren dan kwallon kulob din Manchester City da ke Ingila kuma dan asalin kasar Kwaddebuwa Yaya Toure ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon…

Shahararren dan kwallon kulob din Manchester City da ke Ingila kuma dan asalin kasar Kwaddebuwa Yaya Toure ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC na bana.
Toure ya fafata da ’yan kwallo biyar ne da suka hada da Pierre-Emerick Aubameyang da John Mikel Obi, da bictor Moses da kuma Jonathan Pitroipa.
Sau hudu kenan a jere ake fafafata da Toure a wannan gasa amma sai a bana ya samu nasarar lasheta.
“A gaskiya na yi murnar lashe wannan gasa a wannan lokaci.  Kuma na yi farin cikin ganin yadda ’yan kwallon Afirka suke haskakawa a sassan duniya da nan gaba kadan za su ba duniya mamaki a fagen kwallo”,  inji Toure a lokacin da yake hira da ’yan jaridu jim kadan bayan an bayyana shi a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC a ranar Litinin da ta gabata.
Ita dai gasar kwararru masana harkar kwallo su kimanin 44 ne suke zakulo hazikan ’yan kwallo daga ciki da wajen Afirka don fafatawa a duk shekara.