✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya’yan da matata ta haifa ba nawa ba ne -Tsohon dan kwallon Ghana

Tsohon dan kwallon Ghana Nii Odarty Lamptey ya bayyana cewa ’ya’ya ukun da matarsa mai suna Gloria ta haifa masa bai amince nasa ba ne…

Tsohon dan kwallon Ghana Nii Odarty Lamptey ya bayyana cewa ’ya’ya ukun da matarsa mai suna Gloria ta haifa masa bai amince nasa ba ne bayan an gudanar da binciken jini da ke tantance asalin mahaifin yaran.
Nii, yana daya daga cikin ’yan kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 na Ghana da suka lashe kofin duniya sannan ya taba buga wa kulob din Anderlecht da ke Beljiyam da kuma na Aston billa da ke Ingila kwallo. ya bayyana wa kotu cewa ya dade yana zargin matarsa da laifin yin hulda da maza a waje amma bai taba zaton za ta iya haifar masa ’ya’yan da ba nasa ba don haka ya yanke shawarar yin gwajin jini don tantance gaskiyar al’amari kuma bincike ya tabbatar ’ya’yan ba nasa ba ne.
Sai dai wani rahoton ya ce ana zargin abokinsa na kusa ne ya yi wa matar ciki kuma ta haifi wadannan yara su uku.
 A nata bangaren, Misis Gloria ta bayyana wa kotu cewa akwai lokacin da mijinta ya shawarce  ta da ta je asibiti don a yi mata allurar daukar ciki bayan ta lura ba zai iya haihuwa ba. Sai dai ba ta bayyana wa kotun ko ’ya’yan na mijin ne ko a’a ba.
Su dai ma’auratan ya zuwa wannan lokaci suna da ’ya’ya uku ne da suka hada da Khadija ’yar shekara 19 da Moyesha mai shekara 18 da kuma Latifa mai shekara 7.
Nii Odarty Lamptey ne ya mallaki kungiyar kwallon kafa ta horar da matasa (Academy) a Ghana mai suna Golden Lions Soccer Academy da kuma makarantar Lamp International School. Ya zuwa yanzu kimanin shekara 20 kenan da yin aurensu.
Matar ta nemi kotu ta raba dukiyar mijin biyu kuma a ba ta rabi don ta cigaba da kula da ’ya’yansu tun da mijin ya nemi rabuwa da ita.