✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya’yan kungiyar Magayo Bayan Sule Lamido sun yi azumi da addu’o’i a Jos

kungiyar Matasa Magoya Bayan dan Takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido mai suna Lamido Youth Mobilization of Nigeria, ta shirya taron…

kungiyar Matasa Magoya Bayan dan Takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido mai suna Lamido Youth Mobilization of Nigeria, ta shirya taron addu’o’in neman samun nasara ga dan takarar nata a garin Jos babban birnin Jihar Filato.

Da yake yi wa wakilinmu bayani kan addu’o’in  da suka shirya, Shugaban kungiyar na kasa kuma  kusa a ayarin yakin neman zaben Sule Lamido,  Abdulhadi Abdullahi Sani Cokali ya bayyana cewa sun shirya addu’o’in ne ganin cewa a duk ’yan takarar Shugaban kasar nan a karkashin Jam’iyyar  PDP, babu wanda ya cancanci a ba shi takarar, kamar Alhaji Sule Lamido.

Ya ce  don haka suka shirya addu’o’in bayan sun yi azumin kwana uku da saukar Alkur’ani kan Allah Ya bai wa dan takarar nasu nasara, a zaben da za a yi.

Ya ce Alhaji Sule Lamido shi ne ainihin dan PDP domin  ba ya da sa’a  a PDP kuma mutum ne tsayayye.