✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yayin da Carlos Tebez ya koma Jubentus

Shahararren dan kwallon Manchester City da ke Ingila Carlos Tebez ya koma kulob din Jubentus da ke Italiya a kan Fam miliyan 10.Kamar yadda kafofin…

Shahararren dan kwallon Manchester City da ke Ingila Carlos Tebez ya koma kulob din Jubentus da ke Italiya a kan Fam miliyan 10.
Kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito, dan kwallon zai rika karbar albasbhin Fam miliyan 4 da dubu 600 a shekara.
Tebez, dan kimanin shekara 29, ya koma kulob din City da ke Ingila ne daga kulob din Manchester United.
A shekaru biyun da suka wuce ya yi ta samun sabani a tsakaninsa da tsohon kocin kulob din City Roberto Mancini inda ya yi ta kokarin  canza sheka amma abin ya ci tura sai a wannan lokaci da shi ma koci Mancini ya bar kulob din bayan an sallame shi.
Kulob din bai gabatar da Tebez ga ’yan jarida ba a shekaranjiya Laraba saboda wadansu batu da ba su gama tattaunawa da dan kwallon ba. Amma rahotanni sun tabbatar yarjejeniya a tsakanin kulob din da shi ta kai matsayin kashi 90 daga cikin 100 don haka ana sa ran nan da ’yan kwanaki komai zai daidaita.