Search
Subscribe
Yi maganin warin jikin nan da turare

Yi maganin warin jikin nan da turare

Warin kashi ko warin jiiki, kamar yadda aka fi sani, wani abu ne da mutane ke fuskanta musamman a lokacin zafi. Abubuwa da dama ne ke kawo wannnan warin jikin, wanda ya hada da halittar mutum tun farko da kuma wani lokacin rashin gyaran jiki, kamar yadda ya kamata.

Idan muka dauki rashin gyaran jiki ya hada da rashin yin wanka sosai da kuma rashin yin amfani da turarurruka na shafawa da fesawa.

Wasu mutane ba sanin jikinsu yana fitar da irin wannan warin, don haka basu mayar da hankali wajen daukar matakin da ya kamata.  Ko ma dai menene warin jiki yana cutar da duk wanda ka ke mu’amla da shi.

Ga wasu hanyoyi da ya kamata mai fama da warin jiki ya bi wajen daukar matakin da ya kamata.

1.    Wanka sosai tare da ba wasu sassa na jikin mutum muhimmancin a wajen wankan ta hanyar yin amfani da lemon tsami ko alimin wajen wanke wadansu sassa da suka hada da hammata da sauransu. Irin wannan wankan kuma za a rinka yin sa, kamar sau uku a kullum.

2.    A yawaita aske gashin hammata

3.    A rika shafa turaren hammata

4.    A shafa turaren jiki da na kaya

5.    Da sauran wasu hanyoyi da aka san za su kori warin jiki tare da dawwama cikin kanshi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin