✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yi wa juna addu’a

Barkanmu da sake saduwa a wannan makon.  A  wannan karon, za mu ga dalilai da ya kamata mu yi wa wasu addu’a ba sai lallai…

Barkanmu da sake saduwa a wannan makon.  A  wannan karon, za mu ga dalilai da ya kamata mu yi wa wasu addu’a ba sai lallai wa kan mu ba.

Idan muka koma makon farko cikin binciken mu a kan yin addu’a, za mu ga littafi mai tsarki na nuna mana muhimmancin yin addu’a da kuma albarka da ke tare da ita, shi ya sa yana da kyau wasu ma su samu wannan albarkan ta wurin tunawa da su a duk lokacin da muke yin addu’a. Tunawa ko kuma sa wasu cikin addu’a domin nuna kauna (ba tare da nunawa ko kuma gaya wa wani cewa za ka ko kana yi wa wani addu’a ba), da zuciya daya da ban gaskiya kana kuma bidan nufin Ubangiji bisa bukatun wasu, misali; marasa lafiya, matafiya, makwabta, sugabanen kasa da mazaunan kasar da dai makamantansu ba tare da neman wani ya biya ka ba amma Ubangiji (domin shi Ya san abin da ka keyi Shi kuma ya san zuciyan kowa) abu ne mai karbuwa a gaban Ubangiji.

Sai muyi lura domin littafi mai tsarki bai koya mana yi wa wasu addu’a da kudi ba kamar yadda mutane da dama ke yi a yau. Ubangiji yana bukatar mu mu yi wa juna addu’a don kauna. A lokacin da Yesu Almasihu yana nan duniya yayi warkaswa, ya tada mattattu, ya ciyar da mutane da dama ba tare da neman kudi ko kyautai a wurin jama’a ba amma sabili da kauna, kaunar da ta kai ga mutuwa akan giciye don fansarmu, ai ya kai mu yi koyi da wannan.

A bayyane take idan har muna binciken littafi mai tsarki a koda yaushe, gama littafi mai tsarki jagorace ga duk wanda ke kaunar bincikenta; Zabura 119:105; MaganarKa fitila ce wadda za ta bi da ni, haske ne kuma a kan hanyata. Rashin biciken littafi mai tsarki kwa kan sa mutum ya zama jahili wajen sanin umurnan Ubangiji Allah. (Yusha’u 4:6, Mutanena sun lalace saboda jahilci. Tun da yake sun ?i ilimi, Ni ma na ?i ku da zaman firist ?ina). Zaka iya yin bayaswa ko kyauta ga ikilisiyar Ubangiji, ko ga fasto, ko gwamraye da marayu ko wani da Ruhun Ubangiji ya bisheka, wannan na dauke da albarkun Ubangiji kwarai da gaske, amma ba wai kana neman wani abu daga wurin Ubangiji sai ka bada kudi ko ka karba domin a yi ko kayi wa wani addu’a, wannan ba daidai bane.

Ummurni ne daga wurin Ubangiji cewa mu dinga tunawa da juna cikin addu’a a koyaushe; Afisawa 6:18 “a koyaushe kuna addu’a da ro?o ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matu?ar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu’a”. Yin haka na kara kaunar juna na kuma kawas da sonkai (wato kamar kayi shekara da shekaru kana rokon Ubangiji ya biya maka [naka] bukata, baka tunawa da yan’uwanka, marayu, ko gomraye ba).

Na biye, yin addu’a domin wasu hanyace ta nuna tabbacin kaunar Yesu Almasihu cikin rayuwan mu na masu bi, yin haka kan karfafa rayuwarmu ta ruhaniyya a zaman Ikkilisiya daya cikin Almasihu.

Filibiyawa 2:1-4; In akwai ?arfafawa a cikin Almasihu, in dai da ?arfin rinjaye na ?auna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku, to, albarkacinsu ku cikasa farin cikina da zamanku lafiya da juna, kuna ?aunar juna, nufinku ?aya, ra’ayinku ?aya. Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali’u, kowa yana mai da ?an’uwansa ya fi shi. Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ?an’uwansa ma. Bayan wannan idan muka dauki bukatun wasu gaban Ubangiji, babu shakka albarkunSa zasu kasance tare da mu Zai kuma (ta hanyoyin da sun sha banban da yadda mu ke tsammani) maye mana gurbin abubuwan da muka rasa. Ayuba 42:10 Ubangiji kuwa ya mayar wa Ayuba da dukiyarsa, sa’ad da ya yi addu’a domin abokansa, sai Ubangiji ya mayar masa da ri?in abin da yake da shi da.

Harma magabtanmu, muna yi masu addu’a domin Ubangiji Allah ya sa kaunarSa cikin zukatansu, Ya maye gurbin mugunta da nagarta. Matiyu 5:44;  Amma ni ina gaya muku, ku ?aunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, Luka 6:28;  Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu’a.

Hakannan kuma mukan iya hada kai a zaman Ikkilisiyar Ubangiji, muna yiwa juna addu’a muna kuma yafewa juna don muzo gaban Ubangiji da tsabtar rai, Shi kuwa zai karbi addu’ar mu. Yakubu 5:14-16; In waninku yana rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji. Addu’ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa. Saboda haka, sai ku ri?a bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu’a, don a warkar da ku. Addu’ar mai adalci tana da ?arfin aiki ?warai da gaske.

Idan muka bincika rayuwar Yesu Almasihu har zuwa ga rayuwar almajiransa cikin littafi mai tsarki, zamu ga cewa Yesu ya koyawa almajiransa yin addu’a kuma ya ummurce su da su rika yin addu’a ba fasawa, bayan mutuwarsa da tashinsa zuwa sama, almajiransa basu fasa yin addu’a ba, suna kuma tunawa da juna cikin addu’a a ko da yaushe, cikin jin dadi, tsanani har kurkuku basu fasa yiwa juna addu’a ba, Ayukan Manzani 12:5-17; Sai aka tsare Bitrus a kurkuku, Ikkilisiya kuwa ta himmantu ga ro?on Allah saboda shi… sai ga mala’ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskaka ?akin, sa’an nan mala’ikan ya bugi Bitrus a kwi?i, ya tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi.” Sai kuwa sar?ar ta zube daga hannunsa. Mala’ikan ya ce masa, “Yi ?amara, ka sa takalminka.” Sai ya yi. Sai ya ce masa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.” …Da ya gane haka, ya je gidan Maryamu, uwar Yahaya wanda ake kira Markus, inda aka taru da yawa, ana addu’a.

Zamu ga abubuwan alajibai idan muka hada kai muna yi wa juna addua’a.

Ubangiji Allah Ya bamu ganewa, amin.