Aminiya

Yin sulhu da barayi na nuna gazawar gwamnati – Ali Kwara

Alhaji Ali Kwara

Alhaji Ali Kwara, shahararren mai kama ’yan fashi ne a Arewacin Najeriya. A tattaunawarsa da Aminiya, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wadansu gwamnoni ke yin sulhu da barayi a matsayin hanyar neman maslaha, inda ya ce wannan babban kuskure ne, tunda akwai dokoki a kasar nan:

Ku ne wadanda ke yaki da ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane, ko ka gamsu da yadda wadansu gwamnoni ke yin sulhu da barayin?

ADVERTISEMENT

Gaskiya matsalar nan ta sata da garkuwa da mutane ta dade, ta fi shekara 30 a Arewacin Najeriya, tun daga Damaturu zuwa Babban Gida har ya kara bazuwa zuwa mafi yawan jihohin kasar nan, wani lokaci kisa suke yi na wadanda suka sace. Tunda mutanen nan suna kisan kai bayan karbar kudi a hannun mutane, a ra’ayina ban gamsu da batun sulhu da gwamnonin Arewa ke yi da barayin ba. Domin wannan sulhun me yake nunawa ke nan? Yana nuna cewa gwamnati ta gaza, ta kasa yin aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Sojojinta da ’yan sandanta da ’yan bangarta, dukkansu ba su da amfani ke nan? Ai yin sulhun nan ba wai gaskiya ce a cikin maganar, ba adalci mutum ya shekara fiye da goma yana kama mutane yana tsare su, yana karbar miliyoyin kudi a hannunsu, wadansu ma kashe su yake yi; rana guda a ce an yi masa afuwa, an tara masa kudi wai da sunan sulhu. Shi wanda aka kashe ko aka yi garkuwa da shi aka kwace masa miliyoyin kudinsa a nan wane adalci ka yi masa? Ka ga babu adalcin da ka yi masa.

Kuma abin bakin ciki, in an ce an yi sulhun, bayan kwana kadan sai ka ga sun koma. Ai barawon da ya rika, sata ta samu gindin zama a cikin kwakwalwarsa da wuya ya daina. Shi ya sa ko sun yi za ka ga gobe sun komo amma wanda bai dade cikin satar ba, wannan in an yi sa’a yakan daina.

ADVERTISEMENT

Ko ka gamsu da makaman da barayin ke bayarwa lokacin sulhu?

Ai ba barawon gaske da zai dauki dukkan makamansa ya mika wa hukuma, sai dai ya debo kadan ya mika, ya rike masu karfin. Yanzu Katsina an yi sulhu na daya, sun  dawo an sake yin sulhu, sun sake dawowa. Ka ga Zamfara an ce an yi sulhu da su, ai kwanan nan ka ji an kashe sojoji tara, inda sun ba da makamansu ina za su samu makaman da za su kashe soja?

To yanzu ina mafita ga wannan yanayi?

Tunda kasar nan akwai doka kan kowane al’amari, in mutum ya aikata laifi in an kama shi a hukunta shi daidai da yadda doka ta ce. Ai ko a cikin Alkur’ani Allah Wanda Ya halicci dan Adam, Ya fadi filla-filla cewa duk wanda ya aikata laifi kaza ga hukuncin da ya kamata a yi masa. Allah Ya ce a yi hukunci, kai kuma ka ce a bar su, ai ka ga da sauran aiki. Wato sulhun nan ko masu ba gwamnonin shawara su yi sulhun suna samun ribar kudi daga sulhun da ake yi a wajen gwamnonin, ko kuma dai wata dabara ce ta samun kudi daga gwamnati cikin sauki. Tunda akwai hukunci a Najeriya, in an kama ka da makami, hukuncinka daurin rai-da-rai ne, dan fashi ko duk mutumin da aka samu ya kashe wani, hukuncinsa kisa ne a dokokin Najeriya. Saboda haka babbar matsalar da ke damun kasar nan ita ce akwai masu karya doka akwai kuma wadanda ke hanawa a hukunta masu karya doka. Idan ka ga wadanda ke yin fashi da makami da sata da garkuwa da mutanen nan mafi yawansu jahilai ne, wadansu sun koya sun maida shi sana’arsu ke nan, ya zame musu hanyar cin abincinsu. Dole ne a yi, dole idan dan sanda ya sauya bayanan da aka dauka a kan barawo a hukunta shi, haka alkali in ya saki barawo a hukunta shi; dan siyasar da ya ba da maboya ga barayi ko wani shugaba su ma a hukunta su, haka ma dukkan masu samar musu da makamai a hukunta su. In aka tsaya aka yi haka aka tabbatar da cewa ana aiki da dokokin hana laifuffuka, al’amuran za su yi sauki.

Kuma wata babbar matsala ita ce, wani lokaci alkali zai yanke hukunci wa dan fashi amma gwamnoninmu sai su kasa sa hannu a aiwatar da hukuncin kisan, wannan ma babbar matsala ce. Kuma ya kamata duk wanda yake aikin kama barayi, gwamnati ta bincike shi ko dan sanda ne ko soja ne ko dan banga ne, gwamnati ta bincike shi, ta tantace shi, yaya halinsa, me yake yi? In ba a yi haka ba, wani lokaci barayi ne ke aikin kama barayi. Shi ma kara bata lamarin yake yi amma in za a gyara kasar nan tilas duk wanda ya aikata ba daidai ba a hukunta shi. In kuwa ba haka ba, masifar da za a gani a gaba tana da yawa, don yanzu kabilun da ke satar shanu da yin fashi da garkuwa da mutane sun ninka Fulani yawa. Ka je ka yi bincike a kasar Hausa, har ma da kasar Kudu. Da wuya a yau din nan ka samu gidan da babu barawon waya. In ka kwatanta lamarin sai ka ga an dauki hanya, don haka tilas sai an dauki matakan gyara daga kowace shiyya.

Ya kamata a rika karfafa gwiwar jami’an tsaro kuma in sun yi abin bajinta a yaba musu, a karfafe su. In sun fada tsautsayi a tallafa musu da iyalansu, a tausaya musu a taimake su. Amma ka kama mai laifi yau gobe a sake shi, wannan abu yana ba mu takaici kuma yana kashe azama da kwarin gwiwar masu kama barayin.

Gwamnan Bauchi ya ce za su hada kai da kai don shawo kan matsalar tsaro a jihar, me za ka ce kan wannan?

Bauchi kasata ce, na san lungu da sakon cikinta kuma na san maboyar barayin. Don haka za mu tafi da ’yan sandanmu duk inda suke, duk inda suka buya mu kamo su mu danka wa hukuma. In Allah Ya so daga nan zuwa cikin shekara mai zuwa za ka ji wadannan matsaloli sun yi sauki.