✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yobe za ta bullo da sabon tsarin kula da ilimi  – Dokta Sani Idris

Gwamnatin Jihar Yobe za ta bullo da sabon tsari na bai wa harkar ilimi fiffiko a jihar. Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Muhammad Sani Idris…

Gwamnatin Jihar Yobe za ta bullo da sabon tsari na bai wa harkar ilimi fiffiko a jihar.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dokta Muhammad Sani Idris ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Nguru a karshen makon jiya.

Dokta Sani Idris ya ce kafin zuwan gwamnatin Gwamna Mai Mala gwamnatocin baya sun taka rawar gani a bangaren ilimi, kuma yanzu gwamnatin za ta dora a kai.

Kwamishinan ya ce za a horar da malamai don su kara samun kwarewa saboda a baya Yobe ita ce hedkwatar Gazargamu inda kasashen Afirka suke tinkaho da ita a wajen ilimi.

Ya ce za a bullo da tsari kan kananan yara wajen koya musu ilimin addini ta yadda za su koyi Larabci da Ingilishi cikin kankanen lokaci a ranakun Asabar da Lahadi.

Dokta Sani ya ce ana kuka da ’yan Boko, inda ya kara da cewa duk rashin ilimin addini ne ke kawo haka, “Da sun samu ilimin addini ba za a rika kuka da su ba.”

Ya ce da likita ya yi karatun addini ba zai tafi yajin aiki ya bar majinyata cikin jinya ba.

A cewar Kwamishinan har ila yau, Gwamna Mai Mala Buni ya ce duk wani jami’in gwamnati ya sanya ’ya’yansa a makarantun gwamnati saboda a inganta makarantu da ilimi a Jihar Yobe.