✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunkurin binne surikin Ganduje a masallaci ya tayar da kura

Wasu al’ummar Musulmi sun yi gargadi a kan shirin iyalan tsohon gwamnan jihar Oyo Marigaya Sanata Abiola Ajimobi, na binne shi a cikin masallaci. Tun…

Wasu al’ummar Musulmi sun yi gargadi a kan shirin iyalan tsohon gwamnan jihar Oyo Marigaya Sanata Abiola Ajimobi, na binne shi a cikin masallaci.

Tun da fari dai kakakin mamacin, Bolaji Tunji ya sanar cewa za a binne shi a babban masallacinsa da ke Oke-Ado a garin Ibadan, babban birnin jihar a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni da karfe 12.00 na rana.

Wasu al’ummar Musulmi sun bayyana yunkurin a matsayin haramtacce a Musulunci, inda suka ce hakan ka iya wofantar da masallacin.

Da yake tsokaci bisa lamarin, wani malamin addinin Musulunci a yankin, Ustaz Ibrahim Akinola cewa ya yi, Manzon Allah Sallal Lahu alaihi wa sallama ya hana binne mamata a masallaci, ya hana a gina masallaci a kan kabari, ya kuma la’anci wanda ya yi hakan.

“Manzon Allah ya ce yin haka aiki ne na Yahudu da Nasara.

“Gina masallaci a kan kaburbura ko binne mamata a cikin masallaci, hakan zai sanya mutane yi wa Allah tarayya da waninSa a wajen bauta.

“Mutane za su rika riyawa a zukatansu cewa wadanda aka binne a masallaci suna da wata daraja ta musamman da za ta amfanesu ko kuma ta kare su daga wani abu.

“Wannan tamkar yi wa Allah Madaukakin Sarki abokan tarayya ne”, inji shi.

Ustaz Akinola ya ce kamata ya yi al’ummar Musulmi su kwana da sanin hadarin binne mamata a cikin masallatai, su kuma sani cewa ana gina masallaci ne bisa doron kadaita Allah tare da tsoronSa.

Haka shi ma wani malamin a jihar Oyo, Shaikh Abdallah Qasim, ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa “Al’ummar Musulmin Jihar Oyo da na garin Ibadan ku farka daga barcin da kuke yi .

“Don Allah kada ku binne Sanata Ajumobi a masallaci.

“Kada ku kori Musulmi masallata daga masallacin” kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 27 ga watan Yuni.

Tsohon Gwamnan jihar Oyo Sanata Ishaq Abiola Ajimobi, jigo ne a jam’iyyar APC kana suriki ga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Ya rasu a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni bayan ya yi fama da jinya, kuma iyalansa sun ba da sanarwar za a binne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni.