✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a ba ’yan kwallon Golden Eaglets filaye a Abuja

Kwanan nan ’yan kwallon Golden Eaglets da suka yi nasarar lashe kofin duniya na matasa a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) za su washe da filaye…

Golan Eaglets, Dele AlampasuKwanan nan ’yan kwallon Golden Eaglets da suka yi nasarar lashe kofin duniya na matasa a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) za su washe da filaye a Abuja bayan gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen ba kowanensu fili a babban birnin Tarayya, Abuja, kamar yadda shugabannin kungiyar suka tabbatar a ranar Talatar da ta wuce.
Kocinsu Manu Garba ya ce tuni daukacin ’yan kwallon da masu horar da su suka cike takardun mallakar filayen (forms) bayan da gwamnatin tarayya ta umarce su da yin haka.
Masana harkar kwallo sun rika caccakar gwamnatin tarayya a lokacin da ta bayar da sanarwar ba ’yan kwallon kyautar Naira miliyan biyu, al’amarin da suke ganin kyautar ta yi kadan.  Sun bayar da shawarar kamata ya yi a ce gwamnatin ta hada wa ’yan kwallon kyautar gidaje ko filaye a Abuja kamar yadda aka yi wa ’yan kwallon da suka lashe kofin a shekarar 2007.
Idan za a iya tunawa, gwamnatin tarayya ta raba wa ’yan kwallon kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles filaye a garin Abuja bayan sun lashe kofin Nahiyar Afirka a watan Fabrairun wannan shekara.