Da Dumi Dumi

Za a birne Robert Mugabe a ranar Lahadi

Wata sanarwa da Gwamnatin kasar Zimbabwe ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewar za a birne gawar tsohon shugaban kasar, Marigayi Robert Mugabe a ranar Lahadi mai zuwa, 15 ga watan Satumba 2019.

Marigayi Mugabe, mai shekaru 95 a duniya, ya rasu a ranar 6 ga watan Satumba a kasar Singapore, bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Sanarwar ta kara da cewa za’ayi bikin birne Mugabe a ranar Asabar, a babban filin wasa na kasar, daga bisani kuma a birne shi a ranar Lahadi.

Hukumomi sun bayyana Mugabe a cikin jerin manyan gwarazan kasar, sai dai basu bayyana a inda za’a binne gawar tashi ba. Bisa al’adar kasar dai ana binne gwaraza, wadanda suka yi wa kasa hidima a wani wajen tarihi mai suna National Heroes Acre, a babban birnin kasar na Harare.

ADVERTISEMENT
Share