✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za a ci gaba da ba wa manoma rancen kudi’

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce za a ci gaba ba wa manoma rance, ganin yadda ‘yan Najeriya ke rungumar harkar noma suke kuma cin…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce za a ci gaba ba wa manoma rance, ganin yadda ‘yan Najeriya ke rungumar harkar noma suke kuma cin amfana.

A jawabinsa ga ‘yan Najeria a Ranar Damokradiyya, Buhari ya ce gwamnati za ta farfado da harkar noman auduga da masaku ta hanyan bayar da basuka.

A cewarsa Babban Bankin Najeriya (CBN) zai bayar da basukan ne domin saukaka noma da samar da auduga da kuma shigo da injinan masaku daga ketare.

Kazalika za a ci gaba da samar da ingantaccen takin zamani mai arha, wanda yanzu akwai masana’antunsa 31 a kasar, wadanda kuma ke samar da ayyuka ga ‘yan kasa.

A cewarsa gwamnati na yin iya kokarinta don samar da hanyoyin kauyuka domin saukaka wa manoma fitar da amfanin gona daga yankunansu zuwa manyan tituna da kasuwanni.