✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a daina biyan jihohi kudaden gyaran titunan tarayya

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta ce nan gaba ba za ta sake mayar wa gwamnatocin jihohi kudaden da suka kashe wurin gyaran titunan da ke…

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta ce nan gaba ba za ta sake mayar wa gwamnatocin jihohi kudaden da suka kashe wurin gyaran titunan da ke jihohinsu mallakar gwamnatin tarayya ba.

Minitsan Yada Labarai da Al’adu Lai Mohammed ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa bayan taron da majalisar ta gudanar a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Lai Mohammed ya kuma sanar da cewa Majalisar ta amince da mayar da N148,141,987,000 zuwa jihohi biyar wadanda suka kashe a kan gyaran hanyoyin kafin fara aiki da sabon matakin.

Jihohin da aka mayarwa kudaden dai sun hada da Kuros Riba, wadda ta karbi N18,394,737,000 da Ondo N7,822,147 da Osun N2,468,938,000 da Bayelsa N38,040,564,000 da kuma Ribas wadda ta karbi N78,953,067,000.

Makudan kudade

Ministan ya kara da cewa an mayar wa jihohin kudaden ne bayan da kwamitin da Shugaba Buhari ya kafa ya tabbatar da kammala gyaran hanyoyi da kuma gadaje a cikin shekaru 10 da suka gabata kuma aka tabbatar da karkonsu.

Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta biya jihohi 31 sama da Naira biliyan 500 a fadin kasar.

“Akwai sauran kason da gwamnatin za ta biya wasu jihohin amma daga baya duk jihar da ta gudanar da gyare-gyare a kan titunan gwamnatin tarayya ba za a mai da mata da komi ba.

“Ko da kuwa daga aljihunka za ka biya dole ne a nemi sanya hannun gwamnatin tarayya wanda Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Gidaje za ta bibiya,” Inji Ministan.

Lai Mohammed ya kara da cewa “za a iya tunawa cewa a shekarar 2016, jihohi 36 a fadin kasar sun aiko wa gwamnatin tarayya lissafin kudade masu matukar yawa da suka kashe na gyaran hanyoyin, inda suke bukatar gwamantin ta mayar musu.

“Hakan ya farkar da Shugaban kasa ya kafa wani kwamiti da zai tabbatar da bukatun nasu kuma su tabbatar da gaskiyar ayyukan da suka ce sunyi.

“Kwamitin dai yana dauke da mutane da aka debo daga ma’aikatu daban-daban a karkashin Ministan Ayyuka da Gidaje, Ministocin Ilimi, Sufuri, Kudi da Minista a Ma’aikatar Ayyuka da kuma Shugaban Hukumar Sayar da Kadarorin Gwamnati (BPP) da sauran ma’aikatanta.

“Bayan kammala aikinsa, kwamitin ya ba da shawarar gwamantin tarayya ta mai da wa jihohi 31 N550,364,297,000, bayan sun gamsu cewa an kammala ayyukan da jihohin suka yi ikirarin yi.

“A lokacin ba a tabbatar da jihohi biyar ba wadanda suka hada da Kuros Riba, da Ribas, da Ondo, da Bayelsa da Osun saboda rashin cikakkun takardu”.

‘Ba sabon yunkuri ba ne’

A martanin da ya mayar ta bakin mai magana da yawunsa, Yinka Oyebode, Shugaban Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, ya fada wa wakilin Aminiya cewa gwamnatin tarayya ta bayyana irin wannan kudurin tun a baya.

A cewarsa, “Idan har sabon mataki ne, Kungiyar Gwamnoni ta Najeriya za ta gudanar da taro saboda daukar matsaya a kan lamarin.

“Jihohin da hakan ya shafa za su bayyana ra’ayoyinsu a kai kuma su dauki mataki”. Inji shi.

Kundin Tsarin Mulki

Wani lauya masanin Kundin Tsarin Mulki, Paul Ananaban (SAN), ya ce babu wani bangare a Kundin Tsarin Mulki da ya bukaci a mayar wa wata jiha kudaden da ta kashe wurin gyare-gyaren hanyoyi.

Ya ce, duk wani gwamnan dai zai gudanar da aiki a kan tituna na gwamnatin tarayya dole ne ya yi hakan bisa amincewar gwamantin saboda akwai alamomi da suka bambanta hanyoyin.

“Ba zai yiwu ka yi haka ba tare da amincewar gwamnatin tarayya ba. Abin takaicin shi ne mutanen jihohin gwamnoni kawai suka sani amma ba shugaban kasa ba wurin yin ayyuka”, inji shi.

Matsalar da hanyoyi za su shiga

Shugaban wata kungiyar farar hula mai fafutukar kare hakkokin ‘yan kasa ta fuskar tattalin arziki, Frank Tietie, ya fada wa Aminiya cewa kudurin dakatar da biyan kudaden ba zai taimaki kasar ba saboda zai kara yawan gurbatattun hanyoyi.

A nashi bangaren, Shugaban Cibiyar Demokradiya da Cigaba, Idayat Hassan ta ce, “Wannan yana cikin matakan da gwamnatin ya kamata ta dauka saboda irin mawuyacin halin da ta shiga.

“Wannan batun mayar da kudade wa gwamnatocin jihohi saboda sun yi gyare-gyare a kan tituna mallakin gwamnatin tarayya yana da kamanceceniya da cin hanci da rashawa”.