✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dauki mataki kan masu yada kalaman batanci- Buhari

A safiyar yau Talata yayin gabatar da jawabin samun ‘yancin kan Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnati za ta dauki tsauraran matakai kan…

A safiyar yau Talata yayin gabatar da jawabin samun ‘yancin kan Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnati za ta dauki tsauraran matakai kan ‘yan kasar da ke yada kalaman batanci a shafukan sada zumunta.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabinsa kai tsaye da kafar talabijin kan bikin cika shekaru 59 da samun ‘yancin kan kasar daga turawan mulkin mallaka.

Shugaban ya kara da cewa, “Muna ci gaba da mayar da hankalinmu kan laifukan da ake aikatawa ta yanar gizo da kuma yadda ake yada kalaman nuna kiyayya batanci ta dandalin fasahar zamani.”

Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su kiyaye tare da girmama juna wajen bayyana bacin ransu ko kuma damuwarsu kan shafukan sada zumuntar da ake yadawa.