✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a fafata wasan karshe na damben boksin na Nahiyar Turai

An bayyana cewar ’yan wasan kasar Turkiyya uku sun yi nasarar kaiwa wasan karshe a wasan damben boksin na Nahiyar Turai na ’yan kasa da…

An bayyana cewar ’yan wasan kasar Turkiyya uku sun yi nasarar kaiwa wasan karshe a wasan damben boksin na Nahiyar Turai na ’yan kasa da shekara 22 da ake gudanarwa a birnin Bladikabkaz da ke kasar Rasha

A wasan kusa da karshe bayan karawarsu daga cikin mata akwai Melek Yamak mai nauyin kilo 48, Busenaz Sürmeneli mai nauyin kilo 69, a maza kuwa Tuğrulhan Erdemir mai nauyin 64 sun yi nasarar zuwa wasan karshe.

A yayin da Melek Yamak za ta kara da ’yar kasar Rasha Ekaterina Paltceba domin lashe kambin zinari, Busenaz Sürmeneli za ta fuskanci ’yar kasar Italiya Angela Carini ce.

Shi kuwa Tuğrulhan Erdemir zai fafata ne da dan kasar Rasha Alan Abeb domin lashe kambin zinarin.

Haka dan kasar Turkiyya da aka fitar a wasan kusa da karshe mai suna Hamide Yabuz bayan fafatawarsa da dan kasar Rasha Geliusa Galieba da suka tashi 3-2 ya lashe kambin tagulla.

Kuma mai nauyin kilo 75 Esmanur Koç da aka fitar bayan fafatawa da dan kasar Poland Agata Kacmarska mai kilo fiye da 81 da kuma Sueda Şahin da aka fitar bayan karawa da ’yar kasar Rasha Kristina Tkacheba sun lashe tagulla.

Daga cikin maza kuma mai kilo 81 Bayram Malkan, da aka fitar bayan karawarsa da Sammy Lee ya lashe kambin tagulla.