Search
Subscribe
Za a fara biyan sabon albashin Naira dubu 30 a kowane lokaci – Minista

Ministan Kwadago Chris Ngige

Za a fara biyan sabon albashin Naira dubu 30 a kowane lokaci – Minista

Gwamnatin tarayya a yau Talata ta ce, kaddamar da sabon albashi mafi karanci na Naira dubu 30 da aka yi, an kafa kwamitin da zai tabbatar an fara biyan ma’aikatan sabon tsarin albashin wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu a matsayin doka.

Ministan kwadago Dakta Chris Ngige, ne ya bayyana hakan lokacin da yake amsa tambayoyi game da sabon tsarin albashin.

Ministan bai bayyana lokacin da za a fara biyan albashin ba amma ya ce, a kowane lokaci daga yanzu gwamnati za ta fara biyan sabon tsarin albashin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin