Da Dumi Dumi

Za a fara gasar Polo ta Kasa ta bana a Katsina

Kungiyar Wasan Kwallon  Polo ta Katsina za ta bude kakar wasa ta bana  a ranar 24 ga Agustan nan  a Katsina.

Shugaban Kungiyar kuma Danmadamin Katsina, Alhaji Usman Usman ya shaida wa wakilin Aminiya a Katsina cewa, “Bisa ga al’ada a Katsina ake bude gasar wanda hakan ke bayar da dama ga sauran jihohi su biyo baya.  Kazalika, mun yanke shawarar fara wasan ne daga ranar 24 ga wannan wata da tarurrukan da mukan yi na  shirye-shiryen gasar. Kuma kamar yadda aka sani, a bana ma mun fitar da kwamitoci daban-daban wadanda za su aiwatar da ayyukansu a karkashin babban kwamitin  wanda a yanzu Mataimakin Shugaban Kwamitin, Madawakin Majidadin Katsina Alhaji Sani Lawal BK ke jagoranta don ganin an yi gasar lafiya an kuma kare lafiya.”

“Daga cikin kwamitocin akwai na tsaro, kiwon lafiya, jin dadi da walwala da samar wa bakin ’yan wasa masauki. Kazalika kungiyar ta dukufa wajen gyaran filin wasan da samar da wuraren daure dawaki da wadataccen ruwan sha da sauran abubuwan bukata a lokacin gudanar da gasar,” inji shi.                                                                                                                                                         Kyaftin din Kungiyar Alhaji Abba Kangiwa ya ce shirye-shirye sun yi nisa na karbar bakin ’yan wasa da kungiyoyinsu wadanda za su fafata don cin kofunan da a kan ware domin yin gasa a kansu.  “Muna sa ran zuwan ’yan wasa daga sassan kasar nan wadanda suka yi fice da kuma masu tasowa. Ba mu  fid da ran a bana tsofaffin  ’yan wasa  za su fafata a tsakaninsu ba,” inji shi.

Idan za a iya tunawa shi wasan Polo, marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ne ya kawo shi tun a 1920. Sannan tun daga lokacin da aka kawo wasan, marigayi Sarkin Katsina Sa Usman Nagogo ne ya samu lambar da har bayan ransa ba a samu wanda ya same ta ba, sai daga baya-bayan nan shigowar su Bello Buba, wato mukamin ‘a tara’ (+) domin sai da Sarki Usman ya kai matakin +7 a gasar.

Har yanzu Katsina ce uwa a harkokin wannan gasa sannan Masarautar Katsina ce ke rike da shugancin kungiyar na dindindin domin a yanzu haka, Mai martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir ne ke rike da wannan ragama, wato mukamin da ake kira da Turanci  ‘Life President.’

ADVERTISEMENT

 

 

Share